Nishadi Radio international
Posts
Posted by
Nishadi Radio international
Shugaban majalisar dattawan Najeriya Godswill Akpabio ya roki shugaban Najeriya Bola Tinubu da ya yi hakuri ya bar wa manyan mutane 'yan sandan da ke gadinsu. A yayin zaman majalisun kasar domin gabatar da kudurin kasafin 2026, Akpabio, ya ce wannan mataki na barazana ga tsaron rayukan manyan mutane ciki har da 'yan majalisa.
Posted by
Nishadi Radio international
A ƙasar Syria,akalla membobin kungiyar IS guda biyar ne suka mutu a wasu jerin hare-hare na sama da Amurka ta kai, kamar yadda kungiyar kare hakkin Ɗan adam ta ƙasar ta fitar a yau Asabar, bayan wani hari da ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin Amurka biyu da kuma wani ma’aikaci mai aikin fassara. https://rfi.my/CHet.f
Posted by
Nishadi Radio international
A Jamhuriyar Benin,bayan gabatar da Candide Azanai tsohon minstan tsaro kuma ɗan adawa a kotun Criet a daren jiya juma’a,an tes keyarsa zuwa gidan yari, a cewar lauyoyinsa, ana tuhumarsa da zagon kasa ga gwamnatin Patrice Talon da furta kalamai na nuna goyon bayan ga tawaye.
Posted by
Nishadi Radio international
Nishadi Radio Online rediyo ce ta zamani wadda ke kawo muku labarai, nishadi, waƙoƙi masu daɗi da shirye-shirye na musamman domin al’umma. 🎶 Muna watsa shirye-shirye kai tsaye awa 24 📻 Saurari rediyon mu a kowane lokaci, ko’ina kake 🔔 Kada ka manta ka bi mu domin samun sabbin shirye-shirye
Posted by
Nishadi Radio international
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce Janar Lagbaja ya rasu ranar Talata da dare bayan shafe wani lokaci yana jinya. Tuni shugaba Bola Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga ƴanuwa da rundunar sojin Najeriya. Janar Lagbaja ya mutu yana da shekara 56 a duniya.
Posted by
Nishadi Radio international
Gwamnatin Soji ta Nijar ta rage farashin gas biyo bayan rage farashin fetur da siminti Bayan rage farashin man fetur zuwa Fcfa 499, farashin tan siminti zuwa Fcfa 50,000 , shugaban rikon kwarya Janar Abdourahamane Tiani ya kara daidaita farashin kayayyakin gas a karamin farashi don taimakawa Al'ummar Kasar.
Posted by
Nishadi Radio international
Hukumar Hizba ta jihar Kano ta chafke jarumin Tiktok G-fresh Alameen bisa zargin kalaman batsa a yanar gizo. Jarumin dai ya taba amsa gayyatar hukumar ta Hizba biyo bayan wani bidiyonsa da ya fitar yana salla ba daidai ba. Jarumin ya yiwa hukumar alkawari ya daina duk wani nau'i na tabara a shafukan sada zumunta, sai dai hukumar a wannan karo ta chafke jarumin bisa saba alkawarin da ya yi a baya na daina kalaman batsa a Tiktok.
Posted by
Nishadi Radio international
Taken Najeriya da za a riƙa rerawa Nigeria a yanzu. Shin wanne kuka iya na yanzu ko na da? we hail thee, Our own dear native land, Though tribe and tongue may differ, In brotherhood, we stand, Nigerians all, and proud to serve Our sovereign Motherland. Our flag shall be a symbol That truth and justice reign, In peace or battle honour’d, And this we count as gain, To hand on to our children A banner without stain. O God of all creation, Grant this our one request, Help us to build a nation Where no man is oppressed, And so with peace and plenty Nigeria may be blessed.
Posted by
Nishadi Radio international



























