TINUBU YA YI GADON MATSALOLI BA ZAI IYA WARWARE SU CIKIN SHEKARA ƊAYA BA, IN JI SARKI SUNUSI Mai martaba sarkin Kano na 14 da 16, Malam Sunusi Lamiɗo Sunusi yayi kira ga ƴan Najeriya da su zama masu kykkyawan fata da kyautata zato, domin shugaban ƙasa Tinubu ba zai iya gyara duk matsalolin da ya gada cikin shekara ɗaya ba. Sarki Sunusi ya bayyana haka ne cikin wani jawabi da ya gabatar a wajen babban taron tattalin arziƙi da zuba jari na Jihar Rivers na shekarar 2024 wanda aka gudanar a garin Fatakol, babban birnin Jihar. "Ɓarnar da aka yi a Najeriya shekaru goma da suka gabata ba za su gyaru a wata shida ko shekara ɗaya ba". In ji shi. "Malam Sunusi ya ƙara da cewa hatta wasu wahalhalun da ake fuskanta za su ɗau lokaci wajen shawo kansu game da tattalin arziƙi. Kuma matakan da gwamnati take ɗauka da ke haifar da tsanani kamar cire tallafin man fetur sun zama wajibi ne matuƙar ana son a samu sauƙi a gaba". Cèwar Sarki Muhammadu Sanusi II.
TINUBU YA YI GADON MATSALOLI BA ZAI IYA WARWARE SU CIKIN SHEKARA ƊAYA BA, IN JI SARKI SUNUSI
Mai martaba sarkin Kano na 14 da 16, Malam Sunusi Lamiɗo Sunusi yayi kira ga ƴan Najeriya da su zama masu kykkyawan fata da kyautata zato, domin shugaban ƙasa Tinubu ba zai iya gyara duk matsalolin da ya gada cikin shekara ɗaya ba.
Sarki Sunusi ya bayyana haka ne cikin wani jawabi da ya gabatar a wajen babban taron tattalin arziƙi da zuba jari na Jihar Rivers na shekarar 2024 wanda aka gudanar a garin Fatakol, babban birnin Jihar.
"Ɓarnar da aka yi a Najeriya shekaru goma da suka gabata ba za su gyaru a wata shida ko shekara ɗaya ba". In ji shi.
"Malam Sunusi ya ƙara da cewa hatta wasu wahalhalun da ake fuskanta za su ɗau lokaci wajen shawo kansu game da tattalin arziƙi. Kuma matakan da gwamnati take ɗauka da ke haifar da tsanani kamar cire tallafin man fetur sun zama wajibi ne matuƙar ana son a samu sauƙi a gaba". Cèwar Sarki Muhammadu Sanusi II.

