MARABA DA ZUWA SHUGABAN KASA DAGA ƘUNGIYAR PATE KAWAI


 MARABA DA ZUWA SHUGABAN KASA DAGA ƘUNGIYAR PATE KAWAI


Ƙungiyar Pate Kawai na miƙa gaisuwa tare da barka da zuwa ga Mai Girma Shugaban Ƙasar Tarayyar Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, bisa zuwansa Jihar Bauchi domin ziyarar ta’aziyya kan rasuwar babban malami na duniya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi (R.A.).


Muna bayyana godiyarmu da jin daɗin wannan ziyara wadda ke nuna girmamawa, tausayi da kulawar Shugaban Ƙasa ga al’ummar Bauchi, da kuma irin rawar da marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya taka wajen yaɗa ilimi, addinin Musulunci, tarbiyya, zaman lafiya da haɗin kan al’umma a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.


Sheikh Dahiru Usman Bauchi malami ne abin koyi, jagora na gaskiya, kuma ginshiƙi ne wajen tarbiyyar al’umma. Rashinsa babban gibi ne ga Musulunci da al’umma baki ɗaya.


Ƙungiyar Pate Kawai na addu’ar Allah Ya jiƙan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sanya Aljannar Firdausi ta zama makomarsa. Muna kuma addu’ar Allah Ya bai wa iyalai, almajirai da ɗaukacin al’ummar Musulmi haƙurin jure wannan babban rashi.


Allah Ya ƙara wa Mai Girma Shugaban Ƙasa lafiya, hikima da nasara a jagorancin ƙasa.


Barka da zuwa Jihar Bauchi, Mai Girma Shugaban Ƙasa.


Yusuf Inuwa Barr.

State Co-ordinator Pate Kawai