Posts

Showing posts from December 26, 2025

Ba na tunanin akwai 'yan ta'addar kungiyar ISIS a jihar Sokoto, inda Donald Trump ya ce ya kai hari in ji masanin tsaro, Dr. Audu Bulama Bukarti. Sai dai Dr. Bulama ya ce idan har shugaban na Amurka ya yi nasarar samun 'yan bindiga irinsu Lakurawa da ke yankin Sokoto da Kebbi, to hakan zai zama babbar nasara a yakin da ake yi da 'yan bindiga.

Yanzu-yanzu: Jirgin United Nigeria Airline ya isa tashar Murtala Muhammad dake Legas, domin daukar fasinjan Kano da su ka shafe sama da awanni 3 suna jira. Hotuna daga Muhammad Alfanda.

HALIN DA AKE CIKI A GARIN JABO JIHAR SOKOTO Bayan harin da Amerika ta kaddamar a garin Jabo, an sake gano wani abu mai kama da abin fashewa a wani wuri daban, daga inda na farko ya fado zuwa wannan wurin, kimanin rabin kilomita ne Lokacin da aka fara tono wurin, an hango wani karfe mai kama da abin da ya fashe jiya, sai aka bada shawarar a dakatar da tonon, domin ana kyautata zaton cewa watakila abu ne mai fashewa da bai tashi ba Saboda haka, muna kira ga dukkan al’umma da su guji kusantar wannan wuri, kada su yi kokarin dubawa ko tana komai, su bar wurin gaba daya har sai an tabbatar da jami'an tsaro da suke da fasahar wannan aikin sun ciresa Muna rokon Allah Ya kare 'yan uwanmu, Allah Ya mayar wa Ameirka sharri da makircinta wa Musulmi

Wannan ne karon farko da Amurkan ke kai hari Najeriya da sunan yaƙi da ta'addanci tun bayan da Donald Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin Soji kan ƙasar game da zargin kisan Kiristoci, sai dai wasu ganau daga jihar Sokoto sun ce harin na Amurka ya faru ne a yankin da bashi da tarihin faruwar hare-haren ƴan bindiga kuma ya shafi tarin fararen hular da basu ji ba basu gani ba. Ƙarin bayani: https://rfi.my/CIWD.f