Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), ta sauke Adegboyega Fasasi daga matsayin Babban Jami'in Tsaro na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta maye gurbinsa da Rasheed Atanda Lawal wanda ya kasance Mataimakin Darakta ne a hukumar.