Nishadi Radio international
Posts
Showing posts from December 31, 2025
Posted by
Nishadi Radio international
Yan bindiga sun sace tsohon É—an majalisar jihar Ogun, Moruf Musa, a Ibiade da ke Æ™aramar hukumar Ogun Waterside ta jihar ranar Talata. Musa, wanda ya taÉ“a zama Shugaban Masu Rinjaye na Majalisa daga shekarar 2007 zuwa 2011, an rawaito cewa an kama shi da misalin Æ™arfe 7:00 na yamma yayin da yake gudanar da sallah a cikin masallacin da ke cikin gidansa. Shugaban Æ™aramar hukumar, Ganiyu Odunoiki, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba, inda ya ce an sace shi ne a lokacin sallar Magariba, kuma ’yan bindigar sun harba bindiga a kan hanya yayin da suke guduwa da shi.
Posted by
Nishadi Radio international