Posts

Showing posts from December 20, 2025

Yadda Gwamnatin Gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum ta gwangwaje

YANZU YANZU SHUGABA TINUBU YA SAUKA A BAUCHI

Daga cikin Masallacin Sheikh Dahiru Usman Bauchi an jiran Isowar Shugaba Tinubu

Tsohon gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya gargadi shugabanni da cewa duk wanda ya ci amanar talakawa, zai gamu da fushin Allah ranar Lahira - Karin bayani a sashen sharhi. Hoto: @GovernorObaseki/X

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Godswill Akpabio ya roki shugaban Najeriya Bola Tinubu da ya yi hakuri ya bar wa manyan mutane 'yan sandan da ke gadinsu. A yayin zaman majalisun kasar domin gabatar da kudurin kasafin 2026, Akpabio, ya ce wannan mataki na barazana ga tsaron rayukan manyan mutane ciki har da 'yan majalisa.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ware naira triliyan 15.52 daga cikin naira triliyan 58 na kasafin kudin 2026 da ya gabatar wa majalisar tarayya, domin biyan basussukan da suka yi wa Najeriya katutu.

Za mu kashe naira tiriliyan 5 kan harkokin tsaron Najeriya a 2026 - Shugaba Tinubu

A Æ™asar Syria,akalla membobin kungiyar IS guda biyar ne suka mutu a wasu jerin hare-hare na sama da Amurka ta kai, kamar yadda kungiyar kare hakkin ÆŠan adam ta Æ™asar ta fitar a yau Asabar, bayan wani hari da ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin Amurka biyu da kuma wani ma’aikaci mai aikin fassara. https://rfi.my/CHet.f

A Jamhuriyar Benin,bayan gabatar da Candide Azanai tsohon minstan tsaro kuma É—an adawa a kotun Criet a daren jiya juma’a,an tes keyarsa zuwa gidan yari, a cewar lauyoyinsa, ana tuhumarsa da zagon kasa ga gwamnatin Patrice Talon da furta kalamai na nuna goyon bayan ga tawaye.

Bola Tinubu Ya Kafa Sabon Tsarin Tsaro, Ya Ayyana Kungiyoyi 6 a matsayin 'Yan Ta'adda

Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi magana game da nasarorin Abba Kabir Yusuf, siyasar Najeriya da makomar NNPP a zaben 2027. Karanta bayanin da ya yi a sashen sharhi. Hoto: Saifullahi Hassan|Facebook

MARABA DA ZUWA SHUGABAN KASA DAGA ƘUNGIYAR PATE KAWAI

Jam'iyyar NNPP ta yi taron masu ruwa da tsaki a Abuja.

Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi ta fitar da sanarwar fara duba watan Rajab na 1447. An umarci al'ummar Musulmi su fara duba watan a yau Asabar, 20 ga Disamba, 2025. Watan Rajab ne na 7 a Kalandar Musulunci wanda Sha'aban da Ramadan ke binsa a baya.

Tabbas Yusuf Buhari Ya Haifu Cikin Mahaifinsa