Posts

Showing posts from December 29, 2025

DA DUMI-DUMI: Wutar lantarkin Najeriya ta sake lalacewa a yau Litinin. Shin ko kuna da wutar NEPA yanzu haka a inda kuke? Abba Pantami

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya bada umarnin gyara Makarantar Firamaren garin Tafare da kuma wutar lantarki ga al’ummar garinda ke Karamar Hukumar Alkaleri. Gwamnan ya ba da wannan umarni ne lokacin da al’ummar Tafare suka tsayar da tawagar motocinsa gwamnan a hanyarsa ta zuwa Alkaleri daga garin Duguri inda suka koka kan tsawon lokaci da suka shafe ba tare da wutar lantarki ba, da kuma lalacewar ginin makarantar firamare guda ษ—aya dake Garin. Gwamna Bala Mohammed ya kewaya don duba halin da makarantar ke ciki, tare da nuna damuwa kan mummunan yanayin da ake koyarwa, inda ya umarci ma’aikatar da abin ya shafa da su fara aikin gyara nan take, tare da gina ฦ™arin azuzuwa domin rage cunkoso. Haka kuma, ya umarci hukumomin da suka dace da su gaggauta dawo da wutar lantarki ga al’ummar Tafaren.

'๐˜๐š๐ง ๐๐š๐ง๐ ๐š ๐š ๐ค๐š๐ซ๐š๐ฆ๐š๐ซ ๐ก๐ฎ๐ค๐ฎ๐ฆ๐š๐ซ ๐€๐ฅ๐ค๐š๐ฅ๐ž ๐ง๐š ๐œ๐ข๐ค๐ข๐ง ๐€๐ฅ๐ค๐ก๐š๐ข๐ซ๐ข. Yayin da Gwamnan Jihar Bauchi Sen. Bala Abdulkadir Mohammed ya miฦ™a musu baburan hawa.

Kakakin Rundunar Sojin Saman Najeriya, Ehimen Ejodame, ya ce dakarun rundunar sun yi nasarar kai farmaki mabuyar 'yan ta'adda a tsaunin Turba da sansanin Kachalla Dogo Sule a jihar Zamfara.

Comrade Sabo Muhammad ya bayar da gudummawar Dalar Amurka ษ—ari ($100) domin sayen kujerun zama a Makarantar Sakandaren Jibril Aminu da ke Bauchi, da nufin inganta yanayin koyarwa da koyo a makarantar. Ya sanar da tallafin ne a yayin taron cika shekaru goma (2015–2025) da kammala karatu a makarantar, wani biki da ฦ˜ungiyar Tsofaffin Daliban Makarantar Sakandaren Jibril Aminu ta shirya a Bauchi. Comrade Sabo Muhammad ya bayyana cewa gudummawar na daga cikin ฦ™oฦ™arinsa na tallafa wa ci gaban ilimi da kuma Mara wa Gwamnati baya wajan karfafa ilimi. Shugabannin makarantar da ฦ™ungiyar tsofaffin daliban sun nuna jin daษ—insu bisa wannan tallafi, tare da yin alฦ™awarin amfani da kuษ—in yadda ya dace domin amfanin ษ—alibai da bunฦ™asa harkokin ilimi a makarantar.