Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi ta fitar da sanarwar fara duba watan Rajab na 1447. An umarci al'ummar Musulmi su fara duba watan a yau Asabar, 20 ga Disamba, 2025. Watan Rajab ne na 7 a Kalandar Musulunci wanda Sha'aban da Ramadan ke binsa a baya.
Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi ta sanar da cewa ranar Asabar, 20, Disamba, 2025, ita ce ranar duba watan Rajab na 1447AH An bukaci duk wanda ya ga wata da ya kai rahoto ga masarauta mafi kusa kamar wajen hakimi ko dagaci domin sanar da Sultan Rajab ne wata na bakwai a kalandar Musulunci daga shi kuma sai Sha’aban, sannan Ramadan da Musulmi ke azumi a cikinsa Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. FCT, Abuja - Hukumar da ke kula da harkokin addini a Masarautar Sakoto ta sanar da Musulmi a fadin Najeriya cewa za a fara duba watan Rajab na 1447AH a yau Asabar, 20, Disamba, 2025. A cewa
r sanarwar, ranar da aka kayyade ta yi daidai da 29 ga watan Jumada Assaniya 1447AH. An bukaci Musulmi da su mai da hankali wajen duba watan da zarar rana ta fadi, tare da tabbatar da sahihancin abin da suka gani.