Posts

Shin kana da wayo a lokacin mulkin Obasanjo da Ahmad Mu'azu? Meye zaka iya tunawa da gwamnatinsu?

Hukumar Hizba ta jihar Kano ta chafke jarumin Tiktok G-fresh Alameen bisa zargin kalaman batsa a yanar gizo. Jarumin dai ya taba amsa gayyatar hukumar ta Hizba biyo bayan wani bidiyonsa da ya fitar yana salla ba daidai ba. Jarumin ya yiwa hukumar alkawari ya daina duk wani nau'i na tabara a shafukan sada zumunta, sai dai hukumar a wannan karo ta chafke jarumin bisa saba alkawarin da ya yi a baya na daina kalaman batsa a Tiktok.

Yadda Real Madrid ta lashe Champions League karo na 15 Karin bayani: https://p.dw.com/p/4gXbJ

Gwamnatin jihar Abia da ke kudancin Najeriya ta sanya ladan naira miliyan 25 ga duk wadanda suka bayyana mata maboyar mutanen da suka kashe sojojin Najeriya a jihar. Ya kuke kallon wannan mataki?

Taken Najeriya da za a riƙa rerawa Nigeria a yanzu. Shin wanne kuka iya na yanzu ko na da? we hail thee, Our own dear native land, Though tribe and tongue may differ, In brotherhood, we stand, Nigerians all, and proud to serve Our sovereign Motherland. Our flag shall be a symbol That truth and justice reign, In peace or battle honour’d, And this we count as gain, To hand on to our children A banner without stain. O God of all creation, Grant this our one request, Help us to build a nation Where no man is oppressed, And so with peace and plenty Nigeria may be blessed.

Yanzu haka an yi kwambar motoci a ƙofar Kudu, da ke gidan Sarkin Kano, domin zuwa taro mai martaba sarkin Kano Mallam Muhammadu Suunusi na biyu, zuwa gidan gwamnatin Kano.

TINUBU YA YI GADON MATSALOLI BA ZAI IYA WARWARE SU CIKIN SHEKARA ƊAYA BA, IN JI SARKI SUNUSI Mai martaba sarkin Kano na 14 da 16, Malam Sunusi Lamiɗo Sunusi yayi kira ga ƴan Najeriya da su zama masu kykkyawan fata da kyautata zato, domin shugaban ƙasa Tinubu ba zai iya gyara duk matsalolin da ya gada cikin shekara ɗaya ba. Sarki Sunusi ya bayyana haka ne cikin wani jawabi da ya gabatar a wajen babban taron tattalin arziƙi da zuba jari na Jihar Rivers na shekarar 2024 wanda aka gudanar a garin Fatakol, babban birnin Jihar. "Ɓarnar da aka yi a Najeriya shekaru goma da suka gabata ba za su gyaru a wata shida ko shekara ɗaya ba". In ji shi. "Malam Sunusi ya ƙara da cewa hatta wasu wahalhalun da ake fuskanta za su ɗau lokaci wajen shawo kansu game da tattalin arziƙi. Kuma matakan da gwamnati take ɗauka da ke haifar da tsanani kamar cire tallafin man fetur sun zama wajibi ne matuƙar ana son a samu sauƙi a gaba". Cèwar Sarki Muhammadu Sanusi II.

Domin more kallon hotuna da fayafayen bidiyon da muke wallafawa da ma wasu kayatattun shirye shirye

Wannan su ne cikar ikon masarautar kano. 1- Sandar Mulki 2- Tagwayen Masu 3- Takalmin Jumina

An yaɗa dubban sauro masu yaƙi da Maleriya a Djibouti

Kotu ta Dakatar da Rushe Masarautun Kano

Ƴan wasan England zasu dawo hutun Rabin lokaci Babu suna abayar rigarsu

DUNIYA TUMBIN GIWA Maniyatan aikin haji

A karon farko tun bayan fara yakin Isra’ila da Hamas, mambobin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da gaggauta tsagaita bude wuta a Gaza.

A ranar Laraba aka fara cigiyar Ibrahim Muntaqa Mohammed ɗan shekara shida da ya ɓace, kafin washe gari ƴan sandan jihar Kaduna suka gano gawarsa a yashe da jini a idanunsa da dubura.

Jagorancin Jam'iyyar APC Karkashin Shugaban ta na Kasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje sun ziyarci Shugaba Tinubu yayin da yake hutu a Lagos. 📸 Aminu Dahiru

Soja Ya Kashe Direban Kayan Agaji Kan Na-Goro A Borno

Hare-haren sun faru ne a cikin daren Lahadi da kuma washe gari ranar Kirsimeti a ƙauyukan da ke ƙananan hukumomin Mangu da Bokkos da kuma Barikin Ladi a jihar ta Filato. Karin bayani - https://bbc.in/48t3oKs

SHUGABA TINUBU YA GAGGAUTA DAWO DA DIEZANI NAJERIYA DON A KARBAWA ‘YAN KASA HAKKINSU DAGA GWAMNA DAUDA LAWAL – Anas Abdullahi Kaura Wata gamayyar masu rajin kare jam’iyyar APC ta National Defence ta bukaci gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal da kada ya kawo cikas ga kokarin da tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison-Madueke ke yi na dawowa Najeriya ba tare da wasu kwararan dalilai na zargin aikata ba dai-dai ba. Wannan ne a dai dai lokacin da ake ta cece-kuce a kan batun gudun hijirar da tsohuwar ministar ta yi kan tuhume-tuhume da dama da yaki da masu yiwa tattalin arziki ke yi mata. Alison-Madueke yayin wata zantawa da manema labarai a birnin Landan, ta ce, an zargeta da laifin karkatar da kudi a lokacin da ta ke rike da mukamin ministar man fetur, inda ta ce kuma gaskiya ne, amma ta ce ta son Shugaba Bola Tinubu da ‘yan Najeriya su yafe mata, tare da bata damar dawowa Najeriya da nufin bayar da gudunmawar ciyar da kasar gaba, kasancewar komai na rayuwa wucewa yake. Kungiyar ta yi zargin cewa tsohuwar ministar ta amince tare da danka amana ga gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare, wanda ta ba wa sama da dala biliyan 9 don ya ajiye mata a lokacin da ya rike da mukamin Babban Darakta na First Bank Nigeria PLC. Diezani ta shaida wa manema labarai cewa, mijinta da dukkan ’yan uwanta da lauyanta da ke zaune a Birtaniya sun san dangantakarta da Dauda Lawal Dare, Gwamnan Jihar Zamfara. To sai dai rahotanni sun ambato Diezani na cewa abin takaici, yanzu Dauda Lawal ba ya daukar wayata, har ma yana hada kai da ‘yan sandan Burtaniya su sanya ido a kai na, inda ta yi zargin cewa mai yiwuwa yana kokarin mallakawa kansa kudaden da na ba shi a jiya, idan ba na raye Da yake mayar da martani, kan al’amari shugaban gamayyar masu rajin kare jam’iyyar APC, Kwamred Abdullahi Anas Kaura, ya jaddada muhimmancin bin doka da oda, inda ya bukaci Dauda Lawal Dare da ya guji aikata wani abu da ake ganin zai kawo cikas ga kokarin wanzar da adalci. Cikin wata sanarwar kungiyar ta ce Diezani Alison-Madueke, fitacciyar yar siyasa ce Najeriya, da ke fuskantar zarge-zargen cin hanci da rashawa a lokacin da take rike da mukamin ministar albarkatun man fetur. Diezani Alison-Madueke ta musanta zarge-zargen sannan kuma ta bayyana cewa za ta koma gida Najeriya don warware duk tuhume-tuhume da aka yi mata. Kwamared Kaura ya bukaci a tabbatar da adalci da kuma bin doka da oda, tare da bin dokokin kasa don wanzar da adalci da hakkokin ‘yan kasar, ta yadda za a kwato hakkinsu daga kowaye ba tare da la’akari da mukaminsa ba. Coalition for National Defence ta ce yayin da ake ci gaba da wannan tirkatirka, al’ummar kasar sun sa ido sosai, tare da hankoran yadda za a warware wannan takaddamar da ke tattare da yiwuwar dawowar Diezani da kuma shari’ar da za ta iya biyo baya. Bugu da kari, Kwamared Abdullahi Anas Kaura ya bukaci gwamna Dauda Lawal Dare da ya martabar al’ummar kasa da kuma kimarta a idon duniya. Sannan kuma ya jaddada muhimmancin bin ka’idojin shari’a tare da bai wa hukumomin da suka dace su binciki duk wani zargi da ake yi wa Diezani maimakon kokarin hana ta dawowa ba tare da wani dalili ba. Wannan kiran na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke kokarin karfafa tsarin dimokuradiyya da kuma tabbatar da adalci tare da tunatar da al’umma bukatar hadin kai wajen tunkarar al’amuran da suka shafi kishin kasa. Kwamared Anas kaura ya roki masu kokarin tabbatar da adalci a harkokin shari’a kasancewar daukar kowanne dan kasa dai-dai da kowa a idon shari’a da doka. Bugu-da-kari Kwamared Kaura yace ya yin da al’ummar kasar ke jiran yadda wannan babban al’amarin zai kasance a kotu, akwai bukatar abi doka da ka’idojin shari’a sau da kafa don tabbatar da adalci ga ‘yan kasa.

Wasu fursunoni uku sun tsere daga gidan yari a Ogun Ƙarin bayani - https://bbc.in/4awYfCX

Cristiano Ronaldo, Lionel Messi, Erling Haaland da Luka Modric a yayin da ake cigaba da Bukukuwan Kirsimeti 🎅🎁 • Fagen Wasanni

Me yasa ake yawan zargin wasu daga cikin ministocin Buhari da aikata almundahana da dukiyar kasa da cin hanci ?

Zangon dare

Nishadi radio online

Duniyar wassanni

Sarki Kano na 14, wanda ya nuna takaicin harin bam na 'kuskure' da sojoji suka saki a kan masu Maulidi a Kaduna, ya bukaci mutane da su kai zuciya nesa domin kyale hukumomi su yi aikinsu.

Naira biliyan 15 ne za a kashe domin tafiye-tafiye da abincin Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima a cikin kasafin kudi na 2024 a Najeriya.

Kwamishinan 'yan sadan jihar kano CP muhammed Gumel ya bada umarnin kamo dan sandan daya harbe tsohon dan wasan kwallon kafa nan Smba Player!

Daga kannywood

● duniyar wasanni

Majalisar Koli Kan Harkokin Shari'a ta Najeriya (NJC) ta ce za ta gudanar da bincike kan batutuwan da suka shafi takardun hukuncin zaɓen gwamnan Kano da kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yi.

Zamu amince da bukatan shugaban kasa Tinubu don inganta Najeriya - Tajuden.

Kujeru 300 Kacal Muka Sayar Daga Cikin 6,000 Da Aka Ware Wa Kano

Duniyar wassanni

An ceto ma'aikatan haƙar ma'adanai 41 da suka yi kwana 17 a ƙarƙashin ƙasa

YANZU - YANZU: Shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kudurin kasafin kudinsa na farko ga zaman hadin gwiwar Majalisun Najeriya.