YANZU - YANZU: Shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kudurin kasafin kudinsa na farko ga zaman hadin gwiwar Majalisun Najeriya.
YANZU - YANZU: Shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kudurin kasafin kudinsa na farko ga zaman hadin gwiwar Majalisun Najeriya.
Kasafin kudin na 2024, wanda ya kunshi sama da naira tirliyan 27.5 zai fi mayar da hankali wajen karfafa tsaron kasa da samar da aikin yi da harkokin zuba jari da rage fatara a tsakanin al’umma.
Shugaba Bola Tinubu ya ce an tsara kasafin kudin na shekara mai zuwa ne bisa hasashen sayar da gangar man fetur daya a kan dala 77.96, da hako kiyasin ganga miliyan 1.78 ta man fetur a kullum. Sannan da dalar Amurka daya a kan canjin naira 750.
Kasafin kudin ya yi kudurin kashe naira tirliyan 9.92 a bangaren ayyukan yau da kullum. Sai kuma naira tirliyan 8.25 wajen biyan bashi, yayin da manyan ayyuka za su samu naira tirliyan 8.7.




