Zamu amince da bukatan shugaban kasa Tinubu don inganta Najeriya - Tajuden.

 Zamu amince da bukatan shugaban kasa Tinubu don inganta Najeriya - Tajuden.



Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Honorable Tajuden Abbas ya ce majalisar dokokin ƙasar za ta mara wa shugaban ƙasar baya wajen aiwatar da tsare-tsaren da za su inganta ƙasar.


Yayin da yake gabatar da jawabin godiya a taron kasafin kuɗin ƙasar da shugaba Tinubu ya gabatar wa majalisar, kakakin majalisar ya ce majalisar dokokin ƙasar a shirye take wajen mara wa shugaban ƙasar baya don aiwatar da ayyukan da za su amfani ƙasar


''Musamman tsare-tsaren da za su inganta tattalin arzikin ƙasarmu tare da magance fatara da talauci tsakanin al'umma", in ji shi