Kotu ta Dakatar da Rushe Masarautun Kano


 Kotu ta Dakatar da Rushe Masarautun Kano 


Babbar kotun tarayyar mai zama a Kano ta bayar da umurnin dakatar da gwamnatin Kano daga aiwatar da matakin rushe masarautun jihar.

Wannan mataki ya biyo bayan karar da guda daga cikin manyan hakiman da matakin ya shafa Alh Aminu Babba Dan Agundi Sarkin Dawaki Babba ya shigar a gaban kotu domin kalubalantar matakin rusa masarautu da majalisar dokokin Kano ta yi, wanda gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu na amincewa da kudurin.


Kotun Karkashin Justice AM Liman ta sanya ranar 3 ga watan Yuni domin sauraran karar.


Mene ne ra’ fttyy itayin ku kan wannan turka-turka?