Nishadi Radio international
Posts
Posted by
Nishadi Radio international
Hukumar Hizba ta jihar Kano ta chafke jarumin Tiktok G-fresh Alameen bisa zargin kalaman batsa a yanar gizo. Jarumin dai ya taba amsa gayyatar hukumar ta Hizba biyo bayan wani bidiyonsa da ya fitar yana salla ba daidai ba. Jarumin ya yiwa hukumar alkawari ya daina duk wani nau'i na tabara a shafukan sada zumunta, sai dai hukumar a wannan karo ta chafke jarumin bisa saba alkawarin da ya yi a baya na daina kalaman batsa a Tiktok.
Posted by
Nishadi Radio international
Taken Najeriya da za a riƙa rerawa Nigeria a yanzu. Shin wanne kuka iya na yanzu ko na da? we hail thee, Our own dear native land, Though tribe and tongue may differ, In brotherhood, we stand, Nigerians all, and proud to serve Our sovereign Motherland. Our flag shall be a symbol That truth and justice reign, In peace or battle honour’d, And this we count as gain, To hand on to our children A banner without stain. O God of all creation, Grant this our one request, Help us to build a nation Where no man is oppressed, And so with peace and plenty Nigeria may be blessed.
Posted by
Nishadi Radio international
TINUBU YA YI GADON MATSALOLI BA ZAI IYA WARWARE SU CIKIN SHEKARA ƊAYA BA, IN JI SARKI SUNUSI Mai martaba sarkin Kano na 14 da 16, Malam Sunusi Lamiɗo Sunusi yayi kira ga ƴan Najeriya da su zama masu kykkyawan fata da kyautata zato, domin shugaban ƙasa Tinubu ba zai iya gyara duk matsalolin da ya gada cikin shekara ɗaya ba. Sarki Sunusi ya bayyana haka ne cikin wani jawabi da ya gabatar a wajen babban taron tattalin arziƙi da zuba jari na Jihar Rivers na shekarar 2024 wanda aka gudanar a garin Fatakol, babban birnin Jihar. "Ɓarnar da aka yi a Najeriya shekaru goma da suka gabata ba za su gyaru a wata shida ko shekara ɗaya ba". In ji shi. "Malam Sunusi ya ƙara da cewa hatta wasu wahalhalun da ake fuskanta za su ɗau lokaci wajen shawo kansu game da tattalin arziƙi. Kuma matakan da gwamnati take ɗauka da ke haifar da tsanani kamar cire tallafin man fetur sun zama wajibi ne matuƙar ana son a samu sauƙi a gaba". Cèwar Sarki Muhammadu Sanusi II.
Posted by
Nishadi Radio international





























