Nishadi Radio international
Posts
Latest Posts
Posted by
Nishadi Radio international
ANGA WATAN SHA'ABAN A NIGERIA Mai Martaba Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, CFR, mni, Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, ya ayyana yau Talata, 20 ga Janairu, 2026, a matsayin rana ta farko ta watan Sha’aban, shekarar 1447 bayan Hijira.Wannan na ฦunshe ne a cikin wata sanarwa da Farfesa Sambo Wali Junaidu, Wazirin Sokoto, ya sanya wa hannu.๐จ๐ณ๐ณ๐จ๐ฏ๐ผ๐ด๐จ ๐ฉ๐จ๐ณ๐ฐ๐ฎ๐ฏ๐ต๐จ ๐น๐จ๐ด๐จ๐ซ๐จ๐ต๐
Posted by
Nishadi Radio international
Hukumar Gudanarwar Nishadi radio international , a madadin daukacin ma'aikatanta, na farin cikin taya dukkan jama'a murnar shiga sabuwar shekara ta 2026. Wasu da dama ba su samu damar isowa wannan gabar ba, yayin da wasu ke fama da rashin lafiya. Wasu kuma, sun sha fama da bala'o'in rashin zaman lafiya a garuruwa da yankunansu. Muna fata wannan sabuwar shekara za ta sha bambam da sauran shekarun baya a fannin zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki tare da samun saukin rayuwa. Nishadi Radio na kara baku tabbacin cewa mun yi muku tanadin shirye shirye masu matukar muhimmanci da za su ilmantar, fadakar da kuma nishadantar da ku a duk inda ku ke. Ku dai, ku kasance da mu
Posted by
Nishadi Radio international
Yan bindiga sun sace tsohon ษan majalisar jihar Ogun, Moruf Musa, a Ibiade da ke ฦaramar hukumar Ogun Waterside ta jihar ranar Talata. Musa, wanda ya taษa zama Shugaban Masu Rinjaye na Majalisa daga shekarar 2007 zuwa 2011, an rawaito cewa an kama shi da misalin ฦarfe 7:00 na yamma yayin da yake gudanar da sallah a cikin masallacin da ke cikin gidansa. Shugaban ฦaramar hukumar, Ganiyu Odunoiki, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba, inda ya ce an sace shi ne a lokacin sallar Magariba, kuma ’yan bindigar sun harba bindiga a kan hanya yayin da suke guduwa da shi.
Posted by
Nishadi Radio international
Bankunan Najeriya za su fara cajin harajin tura kuษi na ₦50 kan duk wani kuษi da aka tura da ya kai ₦10,000 ko sama da haka daga ranar 1 ga Janairu, 2026, bisa aiwatar da sabuwar dokar haraji. Bankuna irin su UBA da Access Bank sun sanar da kwastomominsu cewa cajin, wanda ake kira Electronic Money Transfer Levy (EMTL), yanzu za a rika kiran sa harajin stamp, kuma mai aikawa ne zai ษauki nauyin cajin, ba mai karษa ba kamar yadda aka saba a baya. An bayyana cewa tura kuษi ฦasa da ₦10,000, biyan albashi, ko tura kuษi tsakanin asusu a banki ษaya babu su a tsarin cajin. A halin da ake ciki, Shugaban ฦasa Bola Tinubu ya jaddada cewa sabbin dokokin haraji za su fara aiki daga ranar 1 ga Janairu, 2026, kamar yadda aka tsara, yana mai cewa gyaran na da nufin ฦarfafa tsarin kuษi da sauฦaฦa bin doka ga ’yan kasa da ’yan kasuwa, kamar yadda Jaridar Daily Nigerian Hausa ta ruwaito. Shin wane tasiri kuke ganin wannan sabuwar dokar haraji zatayi ga rayuwar ‘yan Najeriya?
Posted by
Nishadi Radio international
๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐ 7 ๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐ Labari marar dadin ji da hukumar kiyaye haddura ta kasa reshen jihar ๐๐จ๐ฆ๐๐ ta tabbatar da rasuwar Ma’aikatan gidan Talabijin na NTA 7 a Jihar Gombe, sun rasa rayukansu ne sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyarsu daga Gombe zuwa Yola. Rahotan ya ce ‘yan jarida bakwai sun rasa rayukansu, inda huษu suka jikkata sakamakon Hatsarin Motar da ya rutsa da su a hanyar Gombe zuwa birnin Yola, jihar Adamawa. Tawagar ฦดan jaridan da ke cikin motar ฦungiyar NUJ reshen jihar Gombe, wanda wasu rahotanni sun ce za su halarci ษaurin auren wani ษan jarida ne lamarin ya rutsa da su a hanya. Allah Ya jikansu da rahama, Ya gafarta musu kurakuransu, Ya kuma ba iyalansu, NUJ da NTA, ‘yan uwansu da abokan aiki haฦurin jure wannan babban rashi. Tabbas an sami babban gibi a wannan bangare. #Punch NewsPaper
Posted by
Nishadi Radio international
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya bada umarnin gyara Makarantar Firamaren garin Tafare da kuma wutar lantarki ga al’ummar garinda ke Karamar Hukumar Alkaleri. Gwamnan ya ba da wannan umarni ne lokacin da al’ummar Tafare suka tsayar da tawagar motocinsa gwamnan a hanyarsa ta zuwa Alkaleri daga garin Duguri inda suka koka kan tsawon lokaci da suka shafe ba tare da wutar lantarki ba, da kuma lalacewar ginin makarantar firamare guda ษaya dake Garin. Gwamna Bala Mohammed ya kewaya don duba halin da makarantar ke ciki, tare da nuna damuwa kan mummunan yanayin da ake koyarwa, inda ya umarci ma’aikatar da abin ya shafa da su fara aikin gyara nan take, tare da gina ฦarin azuzuwa domin rage cunkoso. Haka kuma, ya umarci hukumomin da suka dace da su gaggauta dawo da wutar lantarki ga al’ummar Tafaren.
Posted by
Nishadi Radio international
'๐๐๐ง ๐๐๐ง๐ ๐ ๐ ๐ค๐๐ซ๐๐ฆ๐๐ซ ๐ก๐ฎ๐ค๐ฎ๐ฆ๐๐ซ ๐๐ฅ๐ค๐๐ฅ๐ ๐ง๐ ๐๐ข๐ค๐ข๐ง ๐๐ฅ๐ค๐ก๐๐ข๐ซ๐ข. Yayin da Gwamnan Jihar Bauchi Sen. Bala Abdulkadir Mohammed ya miฦa musu baburan hawa.
Posted by
Nishadi Radio international
Comrade Sabo Muhammad ya bayar da gudummawar Dalar Amurka ษari ($100) domin sayen kujerun zama a Makarantar Sakandaren Jibril Aminu da ke Bauchi, da nufin inganta yanayin koyarwa da koyo a makarantar. Ya sanar da tallafin ne a yayin taron cika shekaru goma (2015–2025) da kammala karatu a makarantar, wani biki da ฦungiyar Tsofaffin Daliban Makarantar Sakandaren Jibril Aminu ta shirya a Bauchi. Comrade Sabo Muhammad ya bayyana cewa gudummawar na daga cikin ฦoฦarinsa na tallafa wa ci gaban ilimi da kuma Mara wa Gwamnati baya wajan karfafa ilimi. Shugabannin makarantar da ฦungiyar tsofaffin daliban sun nuna jin daษinsu bisa wannan tallafi, tare da yin alฦawarin amfani da kuษin yadda ya dace domin amfanin ษalibai da bunฦasa harkokin ilimi a makarantar.
Posted by
Nishadi Radio international
Ba na tunanin akwai 'yan ta'addar kungiyar ISIS a jihar Sokoto, inda Donald Trump ya ce ya kai hari in ji masanin tsaro, Dr. Audu Bulama Bukarti. Sai dai Dr. Bulama ya ce idan har shugaban na Amurka ya yi nasarar samun 'yan bindiga irinsu Lakurawa da ke yankin Sokoto da Kebbi, to hakan zai zama babbar nasara a yakin da ake yi da 'yan bindiga.
Posted by
Nishadi Radio international
HALIN DA AKE CIKI A GARIN JABO JIHAR SOKOTO Bayan harin da Amerika ta kaddamar a garin Jabo, an sake gano wani abu mai kama da abin fashewa a wani wuri daban, daga inda na farko ya fado zuwa wannan wurin, kimanin rabin kilomita ne Lokacin da aka fara tono wurin, an hango wani karfe mai kama da abin da ya fashe jiya, sai aka bada shawarar a dakatar da tonon, domin ana kyautata zaton cewa watakila abu ne mai fashewa da bai tashi ba Saboda haka, muna kira ga dukkan al’umma da su guji kusantar wannan wuri, kada su yi kokarin dubawa ko tana komai, su bar wurin gaba daya har sai an tabbatar da jami'an tsaro da suke da fasahar wannan aikin sun ciresa Muna rokon Allah Ya kare 'yan uwanmu, Allah Ya mayar wa Ameirka sharri da makircinta wa Musulmi
Posted by
Nishadi Radio international
Wannan ne karon farko da Amurkan ke kai hari Najeriya da sunan yaฦi da ta'addanci tun bayan da Donald Trump ya yi barazanar ษaukar matakin Soji kan ฦasar game da zargin kisan Kiristoci, sai dai wasu ganau daga jihar Sokoto sun ce harin na Amurka ya faru ne a yankin da bashi da tarihin faruwar hare-haren ฦดan bindiga kuma ya shafi tarin fararen hular da basu ji ba basu gani ba. ฦarin bayani: https://rfi.my/CIWD.f
Posted by
Nishadi Radio international










