Yan bindiga sun sace tsohon ɗan majalisar jihar Ogun, Moruf Musa, a Ibiade da ke ƙaramar hukumar Ogun Waterside ta jihar ranar Talata. Musa, wanda ya taɓa zama Shugaban Masu Rinjaye na Majalisa daga shekarar 2007 zuwa 2011, an rawaito cewa an kama shi da misalin ƙarfe 7:00 na yamma yayin da yake gudanar da sallah a cikin masallacin da ke cikin gidansa. Shugaban ƙaramar hukumar, Ganiyu Odunoiki, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba, inda ya ce an sace shi ne a lokacin sallar Magariba, kuma ’yan bindigar sun harba bindiga a kan hanya yayin da suke guduwa da shi.

 

Yan bindiga sun sace tsohon ɗan majalisar jihar Ogun, Moruf Musa, a Ibiade da ke ƙaramar hukumar Ogun Waterside ta jihar ranar Talata.


Musa, wanda ya taɓa zama Shugaban Masu Rinjaye na Majalisa daga shekarar 2007 zuwa 2011, an rawaito cewa an kama shi da misalin ƙarfe 7:00 na yamma yayin da yake gudanar da sallah a cikin masallacin da ke cikin gidansa.


Shugaban ƙaramar hukumar, Ganiyu Odunoiki, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba, inda ya ce an sace shi ne a lokacin sallar Magariba, kuma ’yan bindigar sun harba bindiga a kan hanya yayin da suke guduwa da shi.