Rundunar ‘yan sandan Jihar Borno ta tabbatar da samun wani lamari da ake zargin tashin bam ne a Masallacin Jumu'a na Al-Adum da ke Kasuwar Gamboru a birnin Maiduguri.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Borno ta tabbatar da samun wani lamari da ake zargin tashin bam ne a Masallacin Jumu'a na Al-Adum da ke Kasuwar Gamboru a birnin Maiduguri.
A cewar sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sanda, ASP Nahum Kenneth Daso, ya wallafa a shafinsa na Facebook, lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:00 na yamma yayin da ake tsaka da gudanar da sallar Magariba.
Ya ce jami’an sashin lalata abubuwan fashewa na rundunar sun fara gudanar da bincike da share wajen da lamarin ya faru, tare da kulle yankin domin kare lafiyar al’umma, yayin da bincike ke ci gaba don gano hakikanin abin da ya faru.
ASP Daso ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar na kan nazari, kuma za a sanar da karin bayani da zarar an samu ci gaba a binciken.
Ya kuma shawarci al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da kasancewa cikin shiri da taka-tsantsan, kasancewar ayyukan tsaro na ci gaba a yankin.