Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya bada umarnin gyara Makarantar Firamaren garin Tafare da kuma wutar lantarki ga al’ummar garinda ke Karamar Hukumar Alkaleri. Gwamnan ya ba da wannan umarni ne lokacin da al’ummar Tafare suka tsayar da tawagar motocinsa gwamnan a hanyarsa ta zuwa Alkaleri daga garin Duguri inda suka koka kan tsawon lokaci da suka shafe ba tare da wutar lantarki ba, da kuma lalacewar ginin makarantar firamare guda ɗaya dake Garin. Gwamna Bala Mohammed ya kewaya don duba halin da makarantar ke ciki, tare da nuna damuwa kan mummunan yanayin da ake koyarwa, inda ya umarci ma’aikatar da abin ya shafa da su fara aikin gyara nan take, tare da gina ƙarin azuzuwa domin rage cunkoso. Haka kuma, ya umarci hukumomin da suka dace da su gaggauta dawo da wutar lantarki ga al’ummar Tafaren.

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya bada umarnin gyara Makarantar Firamaren garin Tafare da kuma wutar lantarki ga al’ummar garinda ke Karamar Hukumar Alkaleri.


Gwamnan ya ba da wannan umarni ne lokacin da al’ummar Tafare suka tsayar da tawagar motocinsa gwamnan a hanyarsa ta zuwa Alkaleri daga garin Duguri inda suka koka kan tsawon lokaci da suka shafe ba tare da wutar lantarki ba, da kuma lalacewar ginin makarantar firamare guda ɗaya dake Garin.


Gwamna Bala Mohammed ya kewaya don duba halin da makarantar ke ciki, tare da nuna damuwa kan mummunan yanayin da ake koyarwa, inda ya umarci ma’aikatar da abin ya shafa da su fara aikin gyara nan take, tare da gina ƙarin azuzuwa domin rage cunkoso.


Haka kuma, ya umarci hukumomin da suka dace da su gaggauta dawo da wutar lantarki ga al’ummar Tafaren.