Bankunan Najeriya za su fara cajin harajin tura kuɗi na ₦50 kan duk wani kuɗi da aka tura da ya kai ₦10,000 ko sama da haka daga ranar 1 ga Janairu, 2026, bisa aiwatar da sabuwar dokar haraji. Bankuna irin su UBA da Access Bank sun sanar da kwastomominsu cewa cajin, wanda ake kira Electronic Money Transfer Levy (EMTL), yanzu za a rika kiran sa harajin stamp, kuma mai aikawa ne zai ɗauki nauyin cajin, ba mai karɓa ba kamar yadda aka saba a baya. An bayyana cewa tura kuɗi ƙasa da ₦10,000, biyan albashi, ko tura kuɗi tsakanin asusu a banki ɗaya babu su a tsarin cajin. A halin da ake ciki, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya jaddada cewa sabbin dokokin haraji za su fara aiki daga ranar 1 ga Janairu, 2026, kamar yadda aka tsara, yana mai cewa gyaran na da nufin ƙarfafa tsarin kuɗi da sauƙaƙa bin doka ga ’yan kasa da ’yan kasuwa, kamar yadda Jaridar Daily Nigerian Hausa ta ruwaito. Shin wane tasiri kuke ganin wannan sabuwar dokar haraji zatayi ga rayuwar ‘yan Najeriya?


 Bankunan Najeriya za su fara cajin harajin tura kuɗi na ₦50 kan duk wani kuɗi da aka tura da ya kai ₦10,000 ko sama da haka daga ranar 1 ga Janairu, 2026, bisa aiwatar da sabuwar dokar haraji.


Bankuna irin su UBA da Access Bank sun sanar da kwastomominsu cewa cajin, wanda ake kira Electronic Money Transfer Levy (EMTL), yanzu za a rika kiran sa harajin stamp, kuma mai aikawa ne zai ɗauki nauyin cajin, ba mai karɓa ba kamar yadda aka saba a baya.


An bayyana cewa tura kuɗi ƙasa da ₦10,000, biyan albashi, ko tura kuɗi tsakanin asusu a banki ɗaya babu su a tsarin cajin. 


A halin da ake ciki, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya jaddada cewa sabbin dokokin haraji za su fara aiki daga ranar 1 ga Janairu, 2026, kamar yadda aka tsara, yana mai cewa gyaran na da nufin ƙarfafa tsarin kuɗi da sauƙaƙa bin doka ga ’yan kasa da ’yan kasuwa, kamar yadda Jaridar Daily Nigerian Hausa ta ruwaito.


Shin wane tasiri kuke ganin wannan sabuwar dokar haraji zatayi ga rayuwar ‘yan Najeriya?