Gwamnatin Tarayya ta kafe cewa sai an fara aiwatar da sabbin dokokin gyaran haraji a ranar 1 ga Janairu, 2026, tana mai cewa gyare-gyaren an yi su ne da nufin farfado da tattalin arziki da kuma wadata ga 'yan Najeriya.

Shugaban Kwamitin Shugaban ƙasa kan manufofin kuɗi da gyaran haraji, Taiwo Oyedele ne ya bayyana hakan a Legas a Juma'ar da ta gabata.
Oyedele ya ba da wannan tabbacin ne bayan ya gabatar da sabuntawa kan aiwatar da gyaran haraji ga Shugaba Bola Tinubu wanda ke hutun karshen shekara a birnin.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron da ya gudana karkashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu, Taiwo Oyedele wanda ya samu rakiyar Shugaban Hukumar Haraji ta Tarayya (FIRS), Zacchaeus Adedeji, da shugaban Kwamitin Aiwatar da manufofin Haraji na Ƙasa, Joseph Tegbe, ya ce kwamitin a shirye yake ya yi aiki da Majalisar Dokoki ta Ƙasa, ya ƙara da cewa "Kamar yadda kuka sani, akwai huɗu daga cikin waɗannan dokoki, kuma biyu daga cikinsu sun riga sun fara aiki.