Comrade Sabo Muhammad ya bayar da gudummawar Dalar Amurka ɗari ($100) domin sayen kujerun zama a Makarantar Sakandaren Jibril Aminu da ke Bauchi, da nufin inganta yanayin koyarwa da koyo a makarantar. Ya sanar da tallafin ne a yayin taron cika shekaru goma (2015–2025) da kammala karatu a makarantar, wani biki da Ƙungiyar Tsofaffin Daliban Makarantar Sakandaren Jibril Aminu ta shirya a Bauchi. Comrade Sabo Muhammad ya bayyana cewa gudummawar na daga cikin ƙoƙarinsa na tallafa wa ci gaban ilimi da kuma Mara wa Gwamnati baya wajan karfafa ilimi. Shugabannin makarantar da ƙungiyar tsofaffin daliban sun nuna jin daɗinsu bisa wannan tallafi, tare da yin alƙawarin amfani da kuɗin yadda ya dace domin amfanin ɗalibai da bunƙasa harkokin ilimi a makarantar.
Comrade Sabo Muhammad ya bayar da gudummawar Dalar Amurka ɗari ($100) domin sayen kujerun zama a Makarantar Sakandaren Jibril Aminu da ke Bauchi, da nufin inganta yanayin koyarwa da koyo a makarantar.
Ya sanar da tallafin ne a yayin taron cika shekaru goma (2015–2025) da kammala karatu a makarantar, wani biki da Ƙungiyar Tsofaffin Daliban Makarantar Sakandaren Jibril Aminu ta shirya a Bauchi.
Comrade Sabo Muhammad ya bayyana cewa gudummawar na daga cikin ƙoƙarinsa na tallafa wa ci gaban ilimi da kuma Mara wa Gwamnati baya wajan karfafa ilimi.
.jpg)
