Posts

Yan bindiga sun sace tsohon ษ—an majalisar jihar Ogun, Moruf Musa, a Ibiade da ke ฦ™aramar hukumar Ogun Waterside ta jihar ranar Talata. Musa, wanda ya taษ“a zama Shugaban Masu Rinjaye na Majalisa daga shekarar 2007 zuwa 2011, an rawaito cewa an kama shi da misalin ฦ™arfe 7:00 na yamma yayin da yake gudanar da sallah a cikin masallacin da ke cikin gidansa. Shugaban ฦ™aramar hukumar, Ganiyu Odunoiki, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba, inda ya ce an sace shi ne a lokacin sallar Magariba, kuma ’yan bindigar sun harba bindiga a kan hanya yayin da suke guduwa da shi.

Bankunan Najeriya za su fara cajin harajin tura kuษ—i na ₦50 kan duk wani kuษ—i da aka tura da ya kai ₦10,000 ko sama da haka daga ranar 1 ga Janairu, 2026, bisa aiwatar da sabuwar dokar haraji. Bankuna irin su UBA da Access Bank sun sanar da kwastomominsu cewa cajin, wanda ake kira Electronic Money Transfer Levy (EMTL), yanzu za a rika kiran sa harajin stamp, kuma mai aikawa ne zai ษ—auki nauyin cajin, ba mai karษ“a ba kamar yadda aka saba a baya. An bayyana cewa tura kuษ—i ฦ™asa da ₦10,000, biyan albashi, ko tura kuษ—i tsakanin asusu a banki ษ—aya babu su a tsarin cajin. A halin da ake ciki, Shugaban ฦ˜asa Bola Tinubu ya jaddada cewa sabbin dokokin haraji za su fara aiki daga ranar 1 ga Janairu, 2026, kamar yadda aka tsara, yana mai cewa gyaran na da nufin ฦ™arfafa tsarin kuษ—i da sauฦ™aฦ™a bin doka ga ’yan kasa da ’yan kasuwa, kamar yadda Jaridar Daily Nigerian Hausa ta ruwaito. Shin wane tasiri kuke ganin wannan sabuwar dokar haraji zatayi ga rayuwar ‘yan Najeriya?

Da alama za a ๐”‡ibi yan kallo domin Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana cewa zai tsaya takarar kujerar Sanata a Kogi ta Tsakiya a shekarar 2027, kujerar da Sanata Natasha ke rike da ita a yanzu. #LeadershipMatters

๐˜๐€๐ ๐‰๐€๐‘๐ˆ๐ƒ๐€ 7 ๐’๐”๐ ๐‘๐€๐’๐” ๐’๐€๐Š๐€๐Œ๐€๐Š๐Ž๐ ๐‡๐€๐“๐’๐€๐‘๐ˆ๐ ๐Œ๐Ž๐“๐€ Labari marar dadin ji da hukumar kiyaye haddura ta kasa reshen jihar ๐†๐จ๐ฆ๐›๐ž ta tabbatar da rasuwar Ma’aikatan gidan Talabijin na NTA 7 a Jihar Gombe, sun rasa rayukansu ne sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyarsu daga Gombe zuwa Yola. Rahotan ya ce ‘yan jarida bakwai sun rasa rayukansu, inda huษ—u suka jikkata sakamakon Hatsarin Motar da ya rutsa da su a hanyar Gombe zuwa birnin Yola, jihar Adamawa. Tawagar ฦดan jaridan da ke cikin motar ฦ˜ungiyar NUJ reshen jihar Gombe, wanda wasu rahotanni sun ce za su halarci ษ—aurin auren wani ษ—an jarida ne lamarin ya rutsa da su a hanya. Allah Ya jikansu da rahama, Ya gafarta musu kurakuransu, Ya kuma ba iyalansu, NUJ da NTA, ‘yan uwansu da abokan aiki haฦ™urin jure wannan babban rashi. Tabbas an sami babban gibi a wannan bangare. #Punch NewsPaper

Rundunar ฦดan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da faruwar tashin Bam a asibitin ฦ™wararru na Bagudo da ke jihar. Da yake yiwa manema labarai jawabi kakkakin rundunar ฦดan sandan SP Bashir Usman ya ce babu labarin rasa rai kawo yanzu. #rfihausa

DA DUMI-DUMI: Wutar lantarkin Najeriya ta sake lalacewa a yau Litinin. Shin ko kuna da wutar NEPA yanzu haka a inda kuke? Abba Pantami

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya bada umarnin gyara Makarantar Firamaren garin Tafare da kuma wutar lantarki ga al’ummar garinda ke Karamar Hukumar Alkaleri. Gwamnan ya ba da wannan umarni ne lokacin da al’ummar Tafare suka tsayar da tawagar motocinsa gwamnan a hanyarsa ta zuwa Alkaleri daga garin Duguri inda suka koka kan tsawon lokaci da suka shafe ba tare da wutar lantarki ba, da kuma lalacewar ginin makarantar firamare guda ษ—aya dake Garin. Gwamna Bala Mohammed ya kewaya don duba halin da makarantar ke ciki, tare da nuna damuwa kan mummunan yanayin da ake koyarwa, inda ya umarci ma’aikatar da abin ya shafa da su fara aikin gyara nan take, tare da gina ฦ™arin azuzuwa domin rage cunkoso. Haka kuma, ya umarci hukumomin da suka dace da su gaggauta dawo da wutar lantarki ga al’ummar Tafaren.

'๐˜๐š๐ง ๐๐š๐ง๐ ๐š ๐š ๐ค๐š๐ซ๐š๐ฆ๐š๐ซ ๐ก๐ฎ๐ค๐ฎ๐ฆ๐š๐ซ ๐€๐ฅ๐ค๐š๐ฅ๐ž ๐ง๐š ๐œ๐ข๐ค๐ข๐ง ๐€๐ฅ๐ค๐ก๐š๐ข๐ซ๐ข. Yayin da Gwamnan Jihar Bauchi Sen. Bala Abdulkadir Mohammed ya miฦ™a musu baburan hawa.

Kakakin Rundunar Sojin Saman Najeriya, Ehimen Ejodame, ya ce dakarun rundunar sun yi nasarar kai farmaki mabuyar 'yan ta'adda a tsaunin Turba da sansanin Kachalla Dogo Sule a jihar Zamfara.

Comrade Sabo Muhammad ya bayar da gudummawar Dalar Amurka ษ—ari ($100) domin sayen kujerun zama a Makarantar Sakandaren Jibril Aminu da ke Bauchi, da nufin inganta yanayin koyarwa da koyo a makarantar. Ya sanar da tallafin ne a yayin taron cika shekaru goma (2015–2025) da kammala karatu a makarantar, wani biki da ฦ˜ungiyar Tsofaffin Daliban Makarantar Sakandaren Jibril Aminu ta shirya a Bauchi. Comrade Sabo Muhammad ya bayyana cewa gudummawar na daga cikin ฦ™oฦ™arinsa na tallafa wa ci gaban ilimi da kuma Mara wa Gwamnati baya wajan karfafa ilimi. Shugabannin makarantar da ฦ™ungiyar tsofaffin daliban sun nuna jin daษ—insu bisa wannan tallafi, tare da yin alฦ™awarin amfani da kuษ—in yadda ya dace domin amfanin ษ—alibai da bunฦ™asa harkokin ilimi a makarantar.

Gwamnatin Tarayya ta kafe cewa sai an fara aiwatar da sabbin dokokin gyaran haraji a ranar 1 ga Janairu, 2026, tana mai cewa gyare-gyaren an yi su ne da nufin farfado da tattalin arziki da kuma wadata ga 'yan Najeriya.

KAI TSAYE: Daga gidan gwamnatin jihar Bauchi wajen gaisuwar bikin kirsimeti da mabiya addinin Kirista ke kawowa gwamnan jihar Bauchi.

DA DUMI DUMI: Uwar Gidan Gwamnan Jihar Bauchi Hajiya Aisha Bala Mohamed Ta Sauke Press Sakatariyar Ta Murjanatu Musa Maidawa Daga Mukaminta Wannan Sanarwar Yafito ne Daga Offishin Uwar Gidan Gwamnan Jihar Bauchi (OFFICE OF THE FIRST LADY BAUCHI).

Ba na tunanin akwai 'yan ta'addar kungiyar ISIS a jihar Sokoto, inda Donald Trump ya ce ya kai hari in ji masanin tsaro, Dr. Audu Bulama Bukarti. Sai dai Dr. Bulama ya ce idan har shugaban na Amurka ya yi nasarar samun 'yan bindiga irinsu Lakurawa da ke yankin Sokoto da Kebbi, to hakan zai zama babbar nasara a yakin da ake yi da 'yan bindiga.

Yanzu-yanzu: Jirgin United Nigeria Airline ya isa tashar Murtala Muhammad dake Legas, domin daukar fasinjan Kano da su ka shafe sama da awanni 3 suna jira. Hotuna daga Muhammad Alfanda.

HALIN DA AKE CIKI A GARIN JABO JIHAR SOKOTO Bayan harin da Amerika ta kaddamar a garin Jabo, an sake gano wani abu mai kama da abin fashewa a wani wuri daban, daga inda na farko ya fado zuwa wannan wurin, kimanin rabin kilomita ne Lokacin da aka fara tono wurin, an hango wani karfe mai kama da abin da ya fashe jiya, sai aka bada shawarar a dakatar da tonon, domin ana kyautata zaton cewa watakila abu ne mai fashewa da bai tashi ba Saboda haka, muna kira ga dukkan al’umma da su guji kusantar wannan wuri, kada su yi kokarin dubawa ko tana komai, su bar wurin gaba daya har sai an tabbatar da jami'an tsaro da suke da fasahar wannan aikin sun ciresa Muna rokon Allah Ya kare 'yan uwanmu, Allah Ya mayar wa Ameirka sharri da makircinta wa Musulmi

Wannan ne karon farko da Amurkan ke kai hari Najeriya da sunan yaฦ™i da ta'addanci tun bayan da Donald Trump ya yi barazanar ษ—aukar matakin Soji kan ฦ™asar game da zargin kisan Kiristoci, sai dai wasu ganau daga jihar Sokoto sun ce harin na Amurka ya faru ne a yankin da bashi da tarihin faruwar hare-haren ฦดan bindiga kuma ya shafi tarin fararen hular da basu ji ba basu gani ba. ฦ˜arin bayani: https://rfi.my/CIWD.f

Kawo yanzu babu wata ฦ™ungiya da ta ษ—auki alhakin kai wannan harin, da ake kyautata zaton na ฦ™unar baฦ™in wake ne. ฦ˜arin bayani - https://bbc.in/3KPHYRH

Rundunar ‘yan sandan Jihar Borno ta tabbatar da samun wani lamari da ake zargin tashin bam ne a Masallacin Jumu'a na Al-Adum da ke Kasuwar Gamboru a birnin Maiduguri.

Yayin da Hanyar sama da gwamnan Bauchi keyi saura kiris ta kammala. shin zaku iya bayyana yawan hanyoyin da Kauran Daulan Usmaniya ๐‘บ๐’‚๐’๐’‚๐’•๐’‚ ๐‘ฉ๐’‚๐’๐’‚ ๐‘จ๐’ƒ๐’…๐’–๐’๐’Œ๐’‚๐’…๐’Š๐’“ ๐‘ด๐’–๐’‰๐’‚๐’Ž๐’๐’‚๐’… yayi a karamar hukumar ku?

Hotuna: Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a yanzu haka yana kaddamar da jami'an tsaron unguwanni da za su yi aikin samar da tsaro a faษ—in jihar. Rahotanni sun bayyana cewa, za a baiwa jami'an damar rike bindigogi da alburusai inda za su yi aiki a kananan hukumomi 44 na jihar Kano. ๐Ÿ“ธ Bashir Ahmad (X)