Nishadi Radio international
Posts
Posted by
Nishadi Radio international
𝐘𝐀𝐍 𝐉𝐀𝐑𝐈𝐃𝐀 7 𝐒𝐔𝐍 𝐑𝐀𝐒𝐔 𝐒𝐀𝐊𝐀𝐌𝐀𝐊𝐎𝐍 𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐑𝐈𝐍 𝐌𝐎𝐓𝐀 Labari marar dadin ji da hukumar kiyaye haddura ta kasa reshen jihar 𝐆𝐨𝐦𝐛𝐞 ta tabbatar da rasuwar Ma’aikatan gidan Talabijin na NTA 7 a Jihar Gombe, sun rasa rayukansu ne sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyarsu daga Gombe zuwa Yola. Rahotan ya ce ‘yan jarida bakwai sun rasa rayukansu, inda huɗu suka jikkata sakamakon Hatsarin Motar da ya rutsa da su a hanyar Gombe zuwa birnin Yola, jihar Adamawa. Tawagar ƴan jaridan da ke cikin motar Ƙungiyar NUJ reshen jihar Gombe, wanda wasu rahotanni sun ce za su halarci ɗaurin auren wani ɗan jarida ne lamarin ya rutsa da su a hanya. Allah Ya jikansu da rahama, Ya gafarta musu kurakuransu, Ya kuma ba iyalansu, NUJ da NTA, ‘yan uwansu da abokan aiki haƙurin jure wannan babban rashi. Tabbas an sami babban gibi a wannan bangare. #Punch NewsPaper
Posted by
Nishadi Radio international
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya bada umarnin gyara Makarantar Firamaren garin Tafare da kuma wutar lantarki ga al’ummar garinda ke Karamar Hukumar Alkaleri. Gwamnan ya ba da wannan umarni ne lokacin da al’ummar Tafare suka tsayar da tawagar motocinsa gwamnan a hanyarsa ta zuwa Alkaleri daga garin Duguri inda suka koka kan tsawon lokaci da suka shafe ba tare da wutar lantarki ba, da kuma lalacewar ginin makarantar firamare guda ɗaya dake Garin. Gwamna Bala Mohammed ya kewaya don duba halin da makarantar ke ciki, tare da nuna damuwa kan mummunan yanayin da ake koyarwa, inda ya umarci ma’aikatar da abin ya shafa da su fara aikin gyara nan take, tare da gina ƙarin azuzuwa domin rage cunkoso. Haka kuma, ya umarci hukumomin da suka dace da su gaggauta dawo da wutar lantarki ga al’ummar Tafaren.
Posted by
Nishadi Radio international
Comrade Sabo Muhammad ya bayar da gudummawar Dalar Amurka ɗari ($100) domin sayen kujerun zama a Makarantar Sakandaren Jibril Aminu da ke Bauchi, da nufin inganta yanayin koyarwa da koyo a makarantar. Ya sanar da tallafin ne a yayin taron cika shekaru goma (2015–2025) da kammala karatu a makarantar, wani biki da Ƙungiyar Tsofaffin Daliban Makarantar Sakandaren Jibril Aminu ta shirya a Bauchi. Comrade Sabo Muhammad ya bayyana cewa gudummawar na daga cikin ƙoƙarinsa na tallafa wa ci gaban ilimi da kuma Mara wa Gwamnati baya wajan karfafa ilimi. Shugabannin makarantar da ƙungiyar tsofaffin daliban sun nuna jin daɗinsu bisa wannan tallafi, tare da yin alƙawarin amfani da kuɗin yadda ya dace domin amfanin ɗalibai da bunƙasa harkokin ilimi a makarantar.
Posted by
Nishadi Radio international
Ba na tunanin akwai 'yan ta'addar kungiyar ISIS a jihar Sokoto, inda Donald Trump ya ce ya kai hari in ji masanin tsaro, Dr. Audu Bulama Bukarti. Sai dai Dr. Bulama ya ce idan har shugaban na Amurka ya yi nasarar samun 'yan bindiga irinsu Lakurawa da ke yankin Sokoto da Kebbi, to hakan zai zama babbar nasara a yakin da ake yi da 'yan bindiga.
Posted by
Nishadi Radio international
HALIN DA AKE CIKI A GARIN JABO JIHAR SOKOTO Bayan harin da Amerika ta kaddamar a garin Jabo, an sake gano wani abu mai kama da abin fashewa a wani wuri daban, daga inda na farko ya fado zuwa wannan wurin, kimanin rabin kilomita ne Lokacin da aka fara tono wurin, an hango wani karfe mai kama da abin da ya fashe jiya, sai aka bada shawarar a dakatar da tonon, domin ana kyautata zaton cewa watakila abu ne mai fashewa da bai tashi ba Saboda haka, muna kira ga dukkan al’umma da su guji kusantar wannan wuri, kada su yi kokarin dubawa ko tana komai, su bar wurin gaba daya har sai an tabbatar da jami'an tsaro da suke da fasahar wannan aikin sun ciresa Muna rokon Allah Ya kare 'yan uwanmu, Allah Ya mayar wa Ameirka sharri da makircinta wa Musulmi
Posted by
Nishadi Radio international
Wannan ne karon farko da Amurkan ke kai hari Najeriya da sunan yaƙi da ta'addanci tun bayan da Donald Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin Soji kan ƙasar game da zargin kisan Kiristoci, sai dai wasu ganau daga jihar Sokoto sun ce harin na Amurka ya faru ne a yankin da bashi da tarihin faruwar hare-haren ƴan bindiga kuma ya shafi tarin fararen hular da basu ji ba basu gani ba. Ƙarin bayani: https://rfi.my/CIWD.f
Posted by
Nishadi Radio international














