Nishadi Radio international
Posts
Posted by
Nishadi Radio international
Yayin da Hanyar sama da gwamnan Bauchi keyi saura kiris ta kammala. shin zaku iya bayyana yawan hanyoyin da Kauran Daulan Usmaniya ๐บ๐๐๐๐๐ ๐ฉ๐๐๐ ๐จ๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐ด๐๐๐๐๐๐๐ yayi a karamar hukumar ku?
Posted by
Nishadi Radio international
Hotuna: Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a yanzu haka yana kaddamar da jami'an tsaron unguwanni da za su yi aikin samar da tsaro a faษin jihar. Rahotanni sun bayyana cewa, za a baiwa jami'an damar rike bindigogi da alburusai inda za su yi aiki a kananan hukumomi 44 na jihar Kano. ๐ธ Bashir Ahmad (X)
Posted by
Nishadi Radio international
Morocco ta faro gasar lashe kofin nahiyar Afrika da ฦafar dama, bayan da ta samu nasara kan Comoros da ci 2 da nema. ฦan wasan gaba na tawagar Morocco Brahim Diaz ne ya fara jefa kwallo a raga a minti na 55, kafin Ayoub El Kaabi da ya shigo ya ฦara a minti na 74. ๐ธ/Reuters
Posted by
Nishadi Radio international
An Buษe HINSAD General Hospital a Bauchi, An Fara Duba Marasa Lafiya 1,000 Kyauta An buษe wani sabon asibiti mai zaman kansa mai suna HINSAD General Hospital Ltd a garin Bauchi, Jihar Bauchi, domin ฦara inganta harkokin kiwon lafiya da rage raษaษin jinya ga al’umma. Bayan buษe asibitin, shugabannin HINSAD General Hospital sun sanar da fara duba marasa lafiya guda 1,000 (dubu ษaya) kyauta, a matsayin gudummawa ga lafiyar jama’a da kuma tallafa wa marasa galihu.
Posted by
Nishadi Radio international
Jam'iyyar PDP reshen Jihar Jigawa ta yi Allah-wadai da dakatarwar da Kwamitin Amintattu na jam’iyyar ya yi wa tsohon gwamna kuma dattijo a jam'iyyar, Alhaji Sule Lamido, inda suka buฦaci a janye dakatarwar nan take.Jam’iyyar ta ce dakatarwar ba ta da tushe, kuma ba ta dace da ka’idoji da dokokin jam’iyyar ba, tana mai jaddada cewa Sule Lamido jigo ne kuma dattijo wanda ya bayar da gudummawa mai yawa ga jam'iyyar tun kafuwarta.
Posted by
Nishadi Radio international






