MRS: An Sauke Farashin Man Fetur a Jihohin Najeriya, Lita Ta Koma Ƙasa da N740 0 An wallafa 22 Dis 2025 da ƙarfe 4:49 Yamma Daga Sani Hamza wanda ya yi bita Muhammad Malumfashi 3 - tsawon

 

MRS: An Sauke Farashin Man Fetur a Jihohin Najeriya, Lita Ta Koma Ƙasa da N740 0 An wallafa 22 Dis 2025 da ƙarfe 4:49 Yamma Daga  Sani Hamza wanda ya yi bita  Muhammad Malumfashi 3 - tsawon mintuna Matatar Dangote ta fara sayar da man fetur a kan farashin ₦739 kan kowace lita a dukkan gidajen mai na MRS a faɗin Najeriya An sauke farashin ne domin rage wahala ga ’yan Najeriya musamman a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara Matatar Dangote ta gargadi masu ƙoƙarin ƙirƙirar ƙarancin man fetur tare da kira ga hukumomi su ɗauki tsauraran matakai a  - Matatar Dangote ta sanar da fara sayar da litar man fetur, a kan farashin ₦739 a dukkan gidajen mai na kamfanin MRS Oil Nigeria Plc da ke faɗin ƙasar. A cewar sanarwar da kamfanin ya fitar a ranar Lahadi, sabon farashin zai fara aiki a dukkan gidajen man MRS sama da 2,000 a ƙasar, domin tabbatar da cewa rangwamen ya kai ga ’yan Najeriya baki ɗaya.