Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Kimiyya ta Tarayya da ke Azare zuwa Sheikh Dahiru Usman Bauchi University of Health Sciences.Ya sanar da wannan sauyi ne ranar Asabar a garin Bauchi, yayin ziyarar ta'aziyya da ya kai ga iyalai da gwamnatin Jihar ta Bauchi.Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa Sheikh Dahiru Bauchi ya "bayar da ilimi mai amfani ga mutane, kuma shi babban malami ne wanda ya yi aiki tuƙuru bisa hanyar Allah Mai Girma, inda ya riƙa yin wa'azi da huɗubobi da yaɗa ilimi da bayyana mahimmancin yin gaskiya da halaye na gari".
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Kimiyya ta Tarayya da ke Azare zuwa Sheikh Dahiru Usman Bauchi University of Health Sciences.
Ya sanar da wannan sauyi ne ranar Asabar a garin Bauchi, yayin ziyarar ta'aziyya da ya kai ga iyalai da gwamnatin Jihar ta Bauchi.
Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa Sheikh Dahiru Bauchi ya "bayar da ilimi mai amfani ga mutane, kuma shi babban malami ne wanda ya yi aiki tuƙuru bisa hanyar Allah Mai Girma, inda ya riƙa yin wa'azi da huɗubobi da yaɗa ilimi da bayyana mahimmancin yin gaskiya da halaye na gari".
