An Buɗe HINSAD General Hospital a Bauchi, An Fara Duba Marasa Lafiya 1,000 Kyauta An buɗe wani sabon asibiti mai zaman kansa mai suna HINSAD General Hospital Ltd a garin Bauchi, Jihar Bauchi, domin ƙara inganta harkokin kiwon lafiya da rage raɗaɗin jinya ga al’umma. Bayan buɗe asibitin, shugabannin HINSAD General Hospital sun sanar da fara duba marasa lafiya guda 1,000 (dubu ɗaya) kyauta, a matsayin gudummawa ga lafiyar jama’a da kuma tallafa wa marasa galihu.
An Buɗe HINSAD General Hospital a Bauchi, An Fara Duba Marasa Lafiya 1,000 Kyauta
An buɗe wani sabon asibiti mai zaman kansa mai suna HINSAD General Hospital Ltd a garin Bauchi, Jihar Bauchi, domin ƙara inganta harkokin kiwon lafiya da rage raɗaɗin jinya ga al’umma.
Bayan buɗe asibitin, shugabannin HINSAD General Hospital sun sanar da fara duba marasa lafiya guda 1,000 (dubu ɗaya) kyauta, a matsayin gudummawa ga lafiyar jama’a da kuma tallafa wa marasa galihu.
Asibitin yana da cikakkun kayan aiki na zamani tare da ƙwararrun ma’aikatan lafiya da ke ba da kulawa ta musamman ga marasa lafiya, a wani yunƙuri na samar da ingantaccen kiwon lafiya mai sauƙin samu.
Asibitin yana a Inkil Unguwar Magaji, Gombe Road, Bauchi, kuma yana buɗe ƙofa ga dukkan al’umma domin su amfana da wannan dama ta musamman.
Bayanan Asibitin:
Suna: HINSAD General Hospital Ltd
RC: 1778068
Wuri: Inkil Unguwar Magaji, Gombe Road, Bauchi, Bauchi State.
📞 Lambobin Waya:
08036164904

























