Daga Kannywood
An yiwa kannywood Fintikau Kuma Rashin Tsari ne Ya Janyo mana Hakan.
A yanzu dai zamani ake na season films a YouTube, Kuma a kaf kannywood babu film daya karbu kamar Labari na na kamfanin Saira movie amma abun mamaki baikai matsayin kananan season films na kudancin Nigeria ba bari nayi bayani
Kannywood
1- Film din labari na yana iya samun masu kallo 900k zuwa 1m duk sati hakan yaza yazama hero a cikin fina finan Hausa film
2- wannan dalilin yasa aka kasa gama aikin har Yan kallo sun fara korafi akan jan Rai da kullin ake muku
3- a hakan ma film din ya mori director da Kuma marubuci
Nollywood
Film din Campus chronicles
1- karamin film ne da aka tara yara kanana domin Annabel apara itace jarumar film din shekarun ta 19 sai kawayen ta da basu wuce 18-19 ba
2- film din ana haskashi ne a wata karama Kuma sabuwar tashar YouTube Mai suna purple flowers tv, wacce ba su dade da kirkirar ta ba
3- amma sukan Sami viewers sama da 2m a duk sati
4- abun birgewa shine sun kammala wannan film a season 1 tak Kuma episode 9 suka kulle labarin, wlh wlh wlh inda Hausa film suka sami viewers din sai film din ya zama kamar Izzar so, amma su Kam suna kammala labarin sun ajiye yanzu sun dauki wani
Mufa a Hausa film idan labari ya karbu sai a ba matubuci kudi yayita janshi tin ana burge Yan kallo har su koma su tsani film din
Izzar so ya ishemu misali
Tinda ake Hausa film ba,a tabayin film da ake kallo kamar wancan film din dana fada ba duk da sabuwar Tasha ce amma suna da episode da mutum miliyan 8 suka kalla, 8 million fa alaji a episode Daya tak amma sun kammala sun koma Wani Saboda sunsan aiki
Tambayar anan shine
Meyasa Hausa film ba,a kallan mu haka
Sannan shin Jan film ba kangado da muke yana taimakon masana,antar ne kokuma kashe kanmu muke....?
Ku bayyana Ra,ayin ku a comment section
Daga : ✍️ Comrd Nasir Yaro Mai-kyau
Duniyar Fina-finan Hausa
