Jam'iyyar PDP reshen Jihar Jigawa ta yi Allah-wadai da dakatarwar da Kwamitin Amintattu na jam’iyyar ya yi wa tsohon gwamna kuma dattijo a jam'iyyar, Alhaji Sule Lamido, inda suka buƙaci a janye dakatarwar nan take.Jam’iyyar ta ce dakatarwar ba ta da tushe, kuma ba ta dace da ka’idoji da dokokin jam’iyyar ba, tana mai jaddada cewa Sule Lamido jigo ne kuma dattijo wanda ya bayar da gudummawa mai yawa ga jam'iyyar tun kafuwarta.