Nishadi Radio international
Posts
Posted by
Nishadi Radio international
Hotuna: Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a yanzu haka yana kaddamar da jami'an tsaron unguwanni da za su yi aikin samar da tsaro a faɗin jihar. Rahotanni sun bayyana cewa, za a baiwa jami'an damar rike bindigogi da alburusai inda za su yi aiki a kananan hukumomi 44 na jihar Kano. 📸 Bashir Ahmad (X)
Posted by
Nishadi Radio international
Morocco ta faro gasar lashe kofin nahiyar Afrika da ƙafar dama, bayan da ta samu nasara kan Comoros da ci 2 da nema. Ɗan wasan gaba na tawagar Morocco Brahim Diaz ne ya fara jefa kwallo a raga a minti na 55, kafin Ayoub El Kaabi da ya shigo ya ƙara a minti na 74. 📸/Reuters
Posted by
Nishadi Radio international
An Buɗe HINSAD General Hospital a Bauchi, An Fara Duba Marasa Lafiya 1,000 Kyauta An buɗe wani sabon asibiti mai zaman kansa mai suna HINSAD General Hospital Ltd a garin Bauchi, Jihar Bauchi, domin ƙara inganta harkokin kiwon lafiya da rage raɗaɗin jinya ga al’umma. Bayan buɗe asibitin, shugabannin HINSAD General Hospital sun sanar da fara duba marasa lafiya guda 1,000 (dubu ɗaya) kyauta, a matsayin gudummawa ga lafiyar jama’a da kuma tallafa wa marasa galihu.
Posted by
Nishadi Radio international








