Majalisar zartaswar jihar Kano a zamanta na 8 a karkashin jagoranci Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ta amince da muhimman ayyukan raya kasa da inganta rayuwar al'ummar jihar Kano, kamar haka;

 Majalisar zartaswar jihar Kano a zamanta na 8 a karkashin jagoranci Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ta amince da muhimman ayyukan raya kasa da inganta rayuwar al'ummar jihar Kano, kamar haka;



 1. Gina gadar sama da ta kasa a Dangundi akan kudi N15,974,357,204.


 2. Gina gadar sama a Sha tale-talen Tal’udu, akan N15,455,507,265.


 3. Ingantawa hanyoyi tare da gina rufaffun magudanan ruwa a hanyan Jakara - Kwarin -  Gogau, akan N3,360,084,380.


 4. Gina titin Kofar Waika - Unguwar Dabai - Yan Kuje Western Bypass, akan kudi N1,579,755,966.


 5. Gina mahadar Unguwa Uku - Yan awaki - Limawa, akan N1,350,460,874.


 6. Kammala hanyar Kanye - Kabo - Dugabau a karamar hukumar Kabo, akan kudi N820,262,071.


 7. Kammala tare da fadada titin Kofar Dawanau - Kwanar Madugu izuwa hannu biyu, a mataki na biyu,  akan N802,695,617.


 8. Sake bayar da kwangilar aikin gadojin masu tafiyar kafa, a wurare daban-daban a fadin jihar Kano, kan N458,443,067.


 9. Gyaran fitilun kan tituna da fitilu masu bada hannu, dake cikin birni, akan N420,000,000.


 10. Karasa biyan kudin tare da dawo da aiki gadan-gadan na kwangilar gyaran hanyar Kwanar Kwankwaso a karamar hukumar Madobi, akan N200,537,271.


 11. Aikin gyare-gyare a Makarantar Kangararru dake Kiru, akan N107,658,976.


 12. Sayan kayayyaki da magunguna na wannan wata, domin baiwa cibiyoyin kiwon lafiyar jama'a dama samar da tsarin kulada masu hatsari, da mata da yara kyauta a jihar, akan kudi N53,654,223.


 13. Biyan magunguna da sinadarai da kayan masarufi da aka kawo wa asibitin yara na Hasiya Bayero, akan kudi N40,820,564.


 14. Kammala biyan kudin shirin gwamnatin jihar Kano zagaye na Uku na allurar rigakafin cutar mashako, a kananan hukumomi 22, akan kudi N37,005,000.


 15. Sake gina babban dakin Karatu da ya kone a kwalejin nazarin shari'a ta Aminu Kano, akan kudi N56,763,475.


COV/AKT/BMW