Majalisa Ta Gamu da Matsifa Yayin da Mabarata Ke Damunsu da Rokon Kudi

 Majalisa Ta Gamu da Matsifa Yayin da Mabarata Ke Damunsu da Rokon Kudi



Majalisar wakilai ta koka ganin yadda mabarata da maroka ke yawan cika harabar majalisar Isma’il Haruna da ke wakiltar mazabar Toro shi ya bayyana haka yayin zaman majalisar Haruna ya ce marokan na cika musu ofisoshi don rokan kudade wanda hakan ke kawo cikas 


Majalisar Wakilai ta koka kan yadda mabarata ke damunsu a harabar majalisar da kuma cikin ofisoshinsu. 


Dan majalisa mai wakiltar mazabar Toro, Isma’il Haruna ya ce mabarata da maroka sun hana su sakat yayin da su ke ofisoshinsu a majalisar. 


Meye majalisar ke cewa kan mabarata da maroka? 


Haruna ya ce wannan matsalar ta na shafar ayyukansu na al’umma wanda a kullum sai sun ci karo da mabaratan wadanda ke rokon kudade ba kakkautawa. 


Dan majalisar ya bayyana haka ne yayin da ya ke magana a dakin majalisar a jiya Alhamis 26 ga watan Oktoba a Abuja, TheCable ta tattaro. Ya ce wannan matsala ta fara wuce gona da iri ganin cewa aiki su ke zuwa yi ba raba kudade ga wasu maroka ba. 


Ya ce: “Mabaratan su na cika harabar majalisar, mu na ganin mutane daban-daban maroka da mabarata da ke cika mana ofisoshi. “Idan za ka fita daga majalisar, wadannan mutane za su zagaye ka, don kawai su roki kudi ba kakkautawa.” Haruna ya kuma yi korafi kan masu tasi da ke kawo cinkoso a mashigar majalisar wanda ke hana su shige da fice a majalisar. 


Wane martani kakakn majalisar ya yi kan maroka? 


Ya kara da cewa: “Direbobin tasi na ‘Bolt’ da ‘Uber’ su na kawo mana cinkoso a harabar majalisar wanda hakan ke hana mu sakat. “Su na zuwa don sauke fasinjoji da kuma daukar wasu, matsalar su na tsayawa har sai sun samu mai komawa su dauka.” 


Yayin da Haruna ke magana, kakakin majalisar ya dakatar da shi inda ya ce ya kamata ya gabatar a matsayin kuduri ne a gaban majalisar.