Yadda Hukumar Hisba takeyi na kama masu Laifi a jihar Kano yasaɓa Dokar Ƙasa da kuma Addinin Musulunci -Cewar Hamza Nuhu Dantani
Yadda Hukumar Hisba takeyi na kama masu Laifi a jihar Kano yasaɓa Dokar Ƙasa da kuma Addinin Musulunci -Cewar Hamza Nuhu Dantani
A tattaunawar da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta yi da shi, Barista Hamza Nuhu Dantani, ya bayyana cewa salon da hukumar HISBA ta ke amfani da shi wajen kama mutanen da ta ke zargi da aikata fasadi yanzu haka a Jihar Kano, ya saɓawa dokar ƙasa da kuma dokokin addinin musulunci.
A cewar Barista Dantani, "Musulunci ya bayyana cewa ko ƙofar gidan mutum ka je ka yi sallama uku ba a amsa ba to ka juya, ba ace ka shigar masa gida kaitsaye ba, balle har ka shiga da sunan yin kame".
Barista ya kuma ƙara da cewa, an kafa hukumar HISBA ne akan ɗora mutanen da su ka saki layi a kan hanya a matsayin musulmai, dan haka ba ta da hurumin kama mutane a kan kowane irin laifi. "Har wadda ba musulma ba sun kama, ba su da hurumin yin hakan". Cewar Barista.
Barista ya cigaba da cewa dokar ƙasa ba ta ba da hurumin a daki mutum in za a kama shi ba ko da kuwa mai laifi ne. "Haka kuma yadda HISBA ke amfani da maza wajen kama mata ya saɓawa doka da shari'ar addinin musulunci. Sannan kuma sanya waɗanda aka kama a gaban kyamara wannan ma ya saɓawa doka, dan haka, duk wanda aka kama ba bisa ƙa'ida ba ya na da ikon shigar da ƙara ya nemi ƴancinsa bisa take haƙƙinsa na ɗan'ada,".
Ku bayyana mana ra’ayinku.



