Wani rikici da ya ɓarke tsakanin makiyaya da manoma ya yi ajalin manoma 10 da
Wani rikici da ya ɓarke tsakanin makiyaya da manoma ya yi ajalin manoma 10 da makiyaya 2 a ƙauyen Jenuwa na Ƙaramar Hukumar Takum a Jihar Taraba.
Rahotanni sun nuna an kashe manoman ne waɗanda dukkansu ’yan uwan juna ne lokacin da suke hanyarsu ta zuwa gona domin yin girbi a ranar Juma’a.
