Tsohon Shugaban ƙasa, Dakta Goodluck Ebele Jonathan, ya yi kira ga majalisun tarayyar ƙasar nan da su fara aikin yadda za a dakatar da zaɓukan da ake yi ba tare da babban zaɓen ƙasa ba domin haɗe su wuri guda.

Jonathan ya ce idan aka ci gaba da zaɓukan wasu jihohi a lokaci daban da zaɓen gama gari saboda wasu hukunce hukuncen da ɓangaren shari'a ya yi, wata rana za a wayi gari shi kansa zaɓen shugaban ƙasa zai zama lokacin yin sa daban.

A yanzu haka dai zaɓukan gwamnoni a jihohi takwas da suka haɗar da Anambra, da Bayelsa, da Edo, da Ekiti, da  Imo, da Kogi, da Osun da kuma Ondo, ana yinsu ne bayan babban zaɓe na ƙasa saboda hukuncin kotuna. 

Shin yaya kuke kallon wannan kira na tsohon shugaban ƙasa Jonathan wajen haɗe zaɓuka rana ɗaya?

Wane tasiri kuke ganin hakan zai yi wajen inganta harkokin zaɓe a ƙasar nan?