KO KASAN ACHABA TA DAWO, A CIKIN BIRNIN KANO.

 KO KASAN ACHABA TA DAWO, A CIKIN BIRNIN KANO.




Tun bayan takaita Zirga Zirgar babura Masu Kafa Uku (Adaidaita Sahu) da Gwamnatin baya tayi bisa yadda aka Fara Samun wasu Bata Gari na amfani dasu da daddare wajen Aikata muggan laifuka hakan yasa Gwamnati da Hukumar Tsaro ta Jihar Kano suka takaita musu Zirga zirga daga karfe 10 na dare. 


Cikin wani Rahoto da wani dan Jaridar mai daukar Hoto ya wallafa mai suna Abdulwahab Said Ahmad  ya wallafa cewa, a yanzu abunda ke Faruwa a Jihar nan shine sana'ar ACHABA ta DAWO musamman da daddare kuma Akan farata ne daga 10:00 dare har 1:00 na dare. Sukan yi ratse don kaucewa Jamian Tsaro wasu guraren ma hakan suke neman alfarma su wuce.


Akwai bukatar Mahukunta su dubi Lamarin.


📸 #BlueLens