DA DUMI - DUMÍ: JERIN ZARGE - ZARGE 10 DA AKE ZARGIN CEWA AN SAKAWA MUHYI MAGAJI N394M TA HANYAR DA BATA DACE BA

 DA DUMI - DUMÍ: JERIN ZARGE - ZARGE 10 DA AKE ZARGIN CEWA AN SAKAWA MUHYI MAGAJI N394M TA HANYAR DA BATA DACE BA 



A takardun fara sauraren ƙarar zarge-zargen da ake masa mai ɗauke da sa hannun sakataren kotun ɗa'ar ma'aikata da aka fitar a ranar 1ga watan Nuwamba, 2023, ana tuhumar shugaban hukumar yaƙi da cin-hanci da rashawa ta Jihar Kano, Muhyi Magaji Rimin Gado da amfani da kujerarsa ba bisa ƙa'ida ba, haɗi da gaza bayar da cikakkun rubutattun bayanai game da kadarorinsa da abin da ya mallaka, gami da yin ƙarya a cikin bayanan da ya bayar na kadarorin.


ZARGI NA (1):

Muhyi Magaji, a lokacin da ya ke kan matsayin shugaban hukumar yaƙi da cin-hanci da rashawa ta Jihar Kano, kana kuma ma'aikacin gwamnati, a wajajen ko ranar 24 ga watan June, 2022 lokacin da ya gabatar da bayanansa a gaban hukumar ɗa'ar ma'aikata (CCBI) a takarda mai lamba (KNSE 149484), ya bayyana bayanai na ƙarya ta hanyar cirewa da ƙin bayyana lambar asusun ajiya mai lamba: 0010209467 ta bankin Sterling Bank wacce ana amfani da ita tun ranar 2 ga watan Mayu, 2016 wanda hakan ya saɓa da doka sakin layi na 11 cikin baka ta biyu (2) na daftarin farko na kundin tsarin mulkin Nageriya 1999 da aka yi wa kwaskwarima tare da hukunci ƙarƙashin sakin layi na 18 cikin baka ta ɗaya (1) da ta biyu (2) na daftari na biyar a dai wannan kundi.


ZARGI NA (2):

Muhyi Magaji, a lokacin da ya ke matsayin shugaban hukumar yaƙi da cin-hanci da rashawa ta Jihar Kano, kana kuma ma'aikacin gwamnati, a wani lokaci a 2015, 2020, 2022, lokacin da ya gabatar da bayanansa a gaban hukumar ɗa'ar ma'aikata (CCBI) a takarda mai lamba (KNSE 149484), ya gabatar da bayanai na ƙarya ta hanyar cirewa da ƙin bayyana lambar asusun ajiya mai lamba: 1010447759 ta Bankin (UBA) wadda ake amfani da ita tun a ranar 2 ga watan Mayu, 2016 wanda hakan ya saɓa da dokar sakin layi na 11 cikin baka ta biyu (2) na daftari na biyar kashi na ɗaya na kundin tsarin mulkin Nageriya 1999 da aka yi wa kwaskwarima tare da hukunci ƙarƙashin sakin layi na 18 cikin baka ta ɗaya (1) da ta biyu (2) na daftari na biyar a dai wannan kundi.


ZARGI NA (3):

Muhyi Magaji, a lokacin da ya ke matsayin shugaban hukumar yaƙi da cin-hanci da rashawa ta Jihar Kano, kana kuma ma'aikacin gwamnati, a wani lokaci a 2015, 2020, 2022, lokacin da ya gabatar da bayananka a gaban hukumar ɗa'ar ma'aikata (CCBI) a takarda mai lamba (KNSE 149484), ya gabatar da bayanai na ƙarya ta hanyar cirewa da ƙin bayyana lambar asusun ajiya mai lamba: 3088277784 ta bankin (First Bank) wadda ake amfani da ita tun a ranar 2 ga watan Mayu, 2016 wanda hakan ya saɓa da dokar sakin layi na 11 cikin baka ta biyu (2) na daftari na biyar kashi na ɗaya na kundin tsarin mulkin Nageriya 1999 da aka yi wa kwaskwarima tare da hukunci ƙarƙashin sakin layi na 18 cikin baka ta ɗaya (1) da ta biyu (2) na daftari na biyar a dai wannan kundi.


ZARGI NA (4):

Muhyi Magaji, a lokacin da ya ke matsayin shugaban hukumar yaƙi da cin-hanci da rashawa ta Jihar Kano, kana kuma ma'aikacin gwamnati, a ranar 3 ga Janairu, 2020, zuwa 2 ga watan Satumba, 2023 ya karɓi adadin kuɗaɗe kimanin (Naira Miliyan 123, 824, 988.40) a asusun ajiyarsa na Zenith Bank mai lamba: 1006752807 bayan ya bayyana ƙadarorinsa a shekarar 2015 da 2022 wanda hakan ya saɓa da abin da ya ke samu, kyauta ko bashi ya kuma ci karo da tanadin doka sashe na sha biyar cikin baka ta (3) na hukumar ɗa'ar ma'aikata da kotun ɗa'ar aiki na (CAP C15  LFN 2004 da hukunci ƙarƙashin sashe na 23 cikin baka ta (1) da ta (2) a dokar.


ZARGI NA (5):

Muhyi Magaji a lokacin da ya ke matsayin shugaban hukumar yaƙi da cin-hanci da rashawa ta Jihar Kano, kana kuma ma'aikacin gwamnati, a ranar ko wajajen watan Janairu, 2018  zuwa 4 ga Satumba, 2023, ya karɓi adadin kuɗaɗe jimillar (Naira Miliyan 192, 921, 697. 50) bayan ya bayyana kadarorinsa a shekarar 2015 da 2022, wanda hakan ya saɓa da abin da ya ke samu, kyauta ko bashi ya kuma ci karo da tanadin doka sashe na sha biyar cikin baka ta (3) na hukumar ɗa'ar ma'aikata da kotun ɗa'ar aiki na (CAP C15  LFN 2004 da hukunci ƙarƙashin sashe na 23 cikin baka ta (1) da ta (2) a dokar.


ZARGI NA (6):

Muhyi Magaji, a lokacin da ya ke matsayin shugaban hukumar yaƙi da cin-hanci da rashawa ta Jihar Kano, kana kuma ma'aikacin gwamnati, a ranar ko wajajen ranar 4 ga watan Yuli, 2023 ya karɓi saƙon shigar kason kuɗaɗe kimanin (Naira 1,500,000), a asusun ajiyarsa na bankin Sterling mai lamba: 0004851403 daga wani mai suna Baffa Abdullahi Bichi sakataren gwamnatin Jihar Kano, wanda hakan ya ci karo da tanadin doka sashe na sha biyar cikin baka ta (3) na hukumar ɗa'ar ma'aikata da kotun ɗa'ar aiki na (CAP C15  LFN 2004 da hukunci ƙarƙashin sashe na 23 cikin baka ta (1) da ta (2) a dokar.


ZARGI NA (7):

Muhyi Magaji, lokacin da ya ke matsayin shugaban hukumar yaƙi da cin-hanci da rashawa ta Jihar Kano, kana kuma ma'aikacin gwamnati, a ranar 4 ga watan Yuli, 2023 ya karɓi saƙon shigar kason kuɗaɗe kimanin (Naira 4,700,000), a asusun ajiyarsa na bankin Zenith mai lamba: 0004851403 daga wani mai suna Baffa Abdullahi Bichi sakataren gwamnatin Jihar Kano, wanda hakan ya ci karo da tanadin doka sashe na sha biyar cikin baka ta (3) na hukumar ɗa'ar ma'aikata da kotun ɗa'ar aiki na (CAP C15  LFN 2004 da hukunci ƙarƙashin sashe na 23 cikin baka ta (1) da ta (2) a dokar.


ZARGI NA (8):

Muhyi Magaji, a lokacin da ya ke matsayin shugaban hukumar yaƙi da cin-hanci da rashawa ta Jihar Kano, kana kuma ma'aikacin gwamnati, a ranar ko wajajen 19 ga watan Maris, 2021 ya yi amfani da kujerarsa ya shigar da son zuciyarsa inda ya nema tare da fidda kuɗaɗe kimanin (Naira Miliyan 1,766,666.06), a matsayin kuɗin aikin ƙwarewa na aikin bincike na shekara ga kamfanin  Messrs Salihu Maitala & Co daidai da (Naira Dubu 600,000) a shekara inda aka bayar ga kamfanin Messrs Salihu Maitala & Co, wanda hakan ya ci karo da tanadin doka sashe na sha biyar cikin baka ta (3) na hukumar ɗa'ar ma'aikata da kotun ɗa'ar aiki na (CAP C15  LFN 2004 da hukunci ƙarƙashin sashe na 23 cikin baka ta (1) da ta (2) a dai cikin wannan dokar.


ZARGI NA (9):

Muhyi Magaji, a lokacin da ya ke matsayin shugaban hukumar yaƙi da cin-hanci da rashawa ta Jihar Kano, kana kuma ma'aikacin gwamnati, a ranar ko wajajen 19 ga watan Maris, 2021 ya keta ƙa'idar aiki inda ya nema tare da fidda kuɗaɗe kimanin (Naira Miliyan 1,766,666.06), a matsayin kuɗin aikin ƙwarewa na aikin bincike na shekara ga kamfanin  Messrs Salihu Maitala & Co daidai da (Naira Dubu 600,000) a shekara inda aka bayar ga kamfanin Messrs Salihu Maitala & Co, wanda hakan ya ci karo da tanadin doka sashe na sha biyar cikin baka ta (3) na hukumar ɗa'ar ma'aikata da kotun ɗa'ar aiki na (CAP C15  LFN 2004 da hukunci ƙarƙashin sashe na 23 cikin baka ta (1) da ta (2) a dai cikin wannan dokar.


ZARGI NA (10):

Muhyi Magaji, a lokacin da ya ke matsayin shugaban hukumar yaƙi da cin-hanci da rashawa ta Jihar Kano, kana kuma ma'aikacin gwamnati, a ranar ko wajajen ranar 3 ga Janairu, 2018 zuwa ranar 4 ga watan Satumba, 2023 bayan ya bayyana ƙadarorinsa a shekarar 2015 ya karɓi kuɗaɗe kimanin (Naira Miliyan  69, 096, 709.19) a susun ajiyarsa na bankin Sterling mai lamba: 0004851403, wanda hakan ya saɓa da abin da ya ke samu, kyauta ko rance, ya kuma ci karo datanadin doka sashe na sha biyar cikin baka ta (3) na hukumar ɗa'ar ma'aikata da kotun ɗa'ar aiki na (CAP C15  LFN 2004 da hukunci ƙarƙashin sashe na 23 cikin baka ta (1) da ta (2) a dai cikin wannan dokar.