Rahoto
Rashin Tsaro Ke Hana Masu Zuba Hannun Jari Zuwa Arewacin Nijeriya-
-Rahoto
Wani mai sharhi kan al’amuran jama’a, Ahmed Bakare, ya koka da cewa, idan ‘yan bindiga za su iya shiga gari su kashe jami’an ‘yan sanda reshen Jihar Zamfara, to lallai yankin Arewacin kasar nan babu zaman lafiya.
Bakare ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da DAILY POST a Gusau a ranar Juma’a.
Arewacin Nijeriya Cikin Kore
Ya koka da yadda al’amuran tsaro gaba daya a jihar ya zama abin damuwa, da daure kai, da kuma abin kunya, ya kuma yi kira da a samar da ingantaccen tsarin tsaro domin magance tabarbarewar lamarin.
Ya kuma yi nuni da cewa gwamnati mai ci a karkashin Gwamna Dauda Lawal ba za ta iya gudanar da ayyukan ci gaba ba matukar ba zaman lafiya a jihar ba, yayin da ya kuma yi nuni da cewa hatta masu zuba jari na saurin ficewa daga jihar saboda matsalar tsaro.
Ya kai matsayin da ba za mu iya guje wa fuskantar gaskiyar lamarin ba mu gaya wa kanmu gaskiya gwamnatoci a kowane mataki na sane da abubuwan da ke faruwa a Jihar Zamfara, amma suna ganin kamar ba ruwansu da al’amura saboda irin ribar da suke samu daga wadannan munanan ayyuka in ji shi.
Bakare ya jaddada cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba zai iya da’awar ci gaban yankin arewacin kasar nan ba tare da magance wadannan matsalolin tsaro da suke fuskanta ba.
Ina ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu shawara da ya magance matsalar ilimin Almajiri, kamar yadda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi, wanda ya taimaka wajen dinke barakar da ke tsakanin Kiristanci da Musulunci a lokacin mulkinsa.

