yajin aikin da ma'aikatan wutar lantarki ta KEDCO

 An shiga duhu a jihohin Katsina, Kano da Jigawa sakamakon yajin aikin da ma'aikatan wutar lantarki ta KEDCO suka tsunduma a yau


Ma'aikatan kamfanin rarraba wutar lantarki ta shiyar Kano, da ta ƙunshin jihohin Kano, da Katsina da kuma Jigawa wato KEDCO a takaice, sun tsunduma, yajin aiki tare da rufe Ofishinsu a wadannan jihohin.


Kamar yadda Katsina Daily News ta ci karo da wata sanarwar da kamfen wutar lantarkin na KEDCO ya fitar a yau, ya bayyana cewa ma'aikatan nasu, sun mara wa Ƙungiyar ma'aikatan wutar lantarki ta kasa 'National Union of Electricity Employees' (NUEE) baya ne, wajen shiga yajin aikin sakamako, rashin biyan wasu hakkokan Ma'aikatan da suka shafi walwala da jin dadin Ma'aikatan, da aka share kusan sama da shekaru 6 ba tare da an biya su.


Sai dai kamfanin ya bayyana cewa suna fafutukar ganin sun shawo kan matsalar ba tare da jimawa ba



Wasu ma'aikatan kuwa a wasu ofisoshin da suke aiki, sun lillika kwalaye a jikin ofisoshin, inda suke bayya cewa wasu yan fanshon Ƙungiyar wutar lantarkin na