Babban Kotun Shari'ar Musulunci
Babban Kotun Shari'ar Musulunci
da ke Hausawa filin Hoki a Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Abdullahi Halliru ta sanya ranar 7/11/2023 domin ci gaba da sauraran shari'ar da ake yi tsakanin Sadiya Haruna da Abubakar Ibrahim G-Fresh.
A zaman kotun na yau Alhamis lauyan mai ƙara Barista A.B Saka ya roki kotun ta ci gaba da sauraran shari'ar sakamakon rashin zuwan lauyan wanda aka yi ƙara kuma ya bayyanawa kotun cewar waɗanda aka yi karar ba su aiko da wani dalili na rashin zuwa kotun ba.
Kotun ta amince inda ta sanya bakwai ga watan Nuwamba mai kamawa domin ci gaba da shari'ar.
Idan za ku iya tunawa Sadiya Haruna ce ta yi ƙarar mijinta inda ta ke neman ya sauwaƙe mata.

